Ranar daya ga wajen disamba na kowace sheka. Ita ce ranar da majalissar Dunkin duniya ta ware domin kula da masu dauke da cutar Sida.
Kamar kowace jiha, Jihar Zamfara na daga cikin jahohin Najeriya da masu dauke da wannan cuta da kungiyoyin kiyon lafiya su ka fito domin yin gangami domin yaki da wannan cuta mai karye garkuwar jiki. Zmsaca ita hukumar da ke kula da masu dauke da cutar Sida a Jihar Zamfara. Kamar kowace shekara ta wannan Shekarar ma hukumar ta gudanar wannan gagarumin aiki Nata.
Haka Zalika baya ga shirya wannan gangami hukumar ta rabawa masu dauke da wannan cuta, abinci da ya hada shinkafa da makaroci. Tare kudin motar zuwa da dawo, kasancewar masu dauke da cutar sun fito a dukkanin kananan hukumomin Jihar 14.
Da ya ke jawabi a wajen bikin, sabon shugaban hukumar Dr. Hussaini Yakubu, ya yaba da kwazon wadanda ya gada kan wannan matsayi, daga nan ya yi alkawarin cewa gwamnatin Jihar Zamfara a karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, a shirye take domin bunkasa jin dadi da walwalar masu dauke da wannan cuta. Ta hanyar tallafawa rayuwar da kuma aurar da su ga junansu domin kaucewa cigaba da Watsa ta cikin Al'umma. Haka Zalika hukumar karkashin jagorancinsa za ta tashi tsaye domin cigaba da fadakarwa akan yadda za a Kare Kai bayan an kamu da kuma hanyoyin Kare kai daga kamuwar da kuma fadakarwa akan dena kyamar masu dauke da ita, kasancewar kyamar ita kanta ciyo ce babba.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
SSA (New Media)
1-12-2020
