NATIONAL PRODUCTIVITY CENTRE hadin guiwa da leadership and Professional Ethics Consult, sun karamma Hon. Faika M. Ahmad, Mai baiwa Gwamnan Jihar Zamfara shawara akan sha'anin jinkai da tallafawa Al'umma. Hukumar dai ta karrama mai baiwa Gwamnan shawara ne tare da muhimmin mutane da su ke bayar da mummiyar gudummuwa wajen Cigaban Kasa a cikin lungu da sako na kasar nan.
Masu karramawar dai sun bayyana cewa kafin su karrama mutum sai sun tabbatar da cewa ya yi wani abin kirki a cikin Al'umma. A cewarsu sun karrama ta ne akan jajircewar da take yi wajen aikinta, ba tare da nuna kasawa ba.
Wanda wannan kambu zai kara mata azama, tare da kara mata karfin guiwar jajircewa wajen aikin Cigaban Kasa.
Bikin bayar da lambar girman dai ya gudana ne a Nigerian Army Resource Centre da ke babban birnin tarayya Abuja.
