A tarihin jahar Zamfara tun kirkirarta a 1996, ba za a taba mantawa da daminar 2020 ba, domin gidajen mutane da dama da a baya suna tsira, daga ambaliyar ruwa amma a wannan Shekarar sun fuskanci wannan matsalar ta ambaliyar ruwa Wanda hakan ya Kara fito da babbar matsalar rashin magudanun ruwan da jahar Zamfara ke cigaba da fama da matsalar da ita. Wanda hakan ya Kara faruwa ne saboda yawan ruwan saman da aka samu a cikin wannan shekara ta 2020 Wanda abin da ba jahar Zamfara kurrum abin ya faru ba. Domin jahohin Sokoto da Kebbi sun fuskanci fiye da wannan matsalar ta ambaliyar ruwa da jahar Zamfara ta fuskanta. Domin jahar Sokoto kurrum kananan hukumomin jahar 11 ne su ka fuskanci ambaliyar ruwa ciki har da rasa rayukkan Al'umma.
MATSALAR GWAMNATIN MATAWALLE TA KAWO TA KO MAGABATANSA?
Matsalar rashin magudanun ruwa da jahar Zamfara ke fuskanta musamman garin Gusau, Da Yan adawa su ka Fara amfani da ita wajen sukar Mai girma Gwamna na cewa ya Kyale garin garin Gusau.
Maganar gaskiya garin Gusau na matukar bukatar magudanun ruwa, kuma wannan ya samo asali ne, saboda rashin tsari Mai kyau da gwamnonin da su ka mulki jahar su ka Dora jahar akai. Domin in ka debe kwaryar garin Gusau (tsofaffin unguwannin cikin garin Gusau) . Dukkanin sabbin unguwannin garin suna fama da matsalar ambaliyar, ruwa. Haka Zalika dukanin garin Gusau ba titi daya da ke da tsayayyar magudanar ruwan da duk ruwan da aka yi a garin ba za su hau titi tare da kwarara a cikin gidajen mutane ba.
WADANNE AYUKKAN TITITUNA NE MAI GIRMA GWAMNA YA YI A CIKIN GARIN GUSAU?
Duk da kalubalen da Mai Daraja Gwamna ya fuskanta na karbar jahar a hagun a hannun wadanda Ya gaji jahar, na mummunan bashi da su ka jefa jahar ciki tare karyewar tattalin arziki da kuma annobar Coronavirus, Hakan bai hana Gwamnan kammala Titin Masallacin Jumu'a na Kanwurin Sarki Gusau, Titin Sabon gari Masallacin yarbawa zuwa Sabon gari ya bullo Sardauna Bread zuwa tankin ruwa ba, tare da Titin bayan Gusau Hotel da kuma na bayan Tsohowar Tasha ba. Da sauran su, Wanda tuni an kammala wadannan Titituna da ake cigaba da Shinfidawa a lungu da sako na jahar Zamfara.
DOLE SAI AL'UMMA SU MA SUN RIKA.
Duk da haka dole Sai Al'ummarmu sun rungumi dabi'ar zabtace magudanun ruwan tare da dena rubar da shara cikin magudannun ruwan tare da yashe su.
WANE TANADI GWAMMAN YA YI WA MATSALAR?
Dan haka matsalar shi kansa Mai girma Gwamna ya gajeta ne, kuma kamar yadda ya bayyana a Bakinsa a cikin shirin A fada a cika na BBC HAUSA a makon da ya wuce, cewa yana daga cikin manyan matsalolin da ya ke son kasancewa. Dan haka muna Kira ga Al'ummar jahar Zamfara da su cigaba da yiwa Mai girma Gwamna uzuri ba zai iya magance dukkan matsalolin jahar Zamfara a shekara daya da watanni ukun da ya yi kan karagar mulki ba, Sai dai Muna neman a cigaba da taya shi da addu'a domin ganin cewa ya magance manyan matsalolin da ke damuwar jahar.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
SSA (New Media)
State Coordinator Belmat Na Sallama
3/9/2020

