Mai daraja gwamnan jahar Zamfara, Hon Dr Bello Mohammed Matawalle (Matawallen Maradun) ya bar kasar nan yau Lahadi 16/06/2019 zuwa kasar saudiya Domin gudanar Da ibadar umura
Gwamnan ya bar kasar nan a cikin jirgin kamfanin Emirates Air a filin jirgin Nnamdi Azikwe International Airport, da ke Abuja zuwa Madinah. Gwamnan na tare da Mai dakinsa Hajiya Aisha Bello Mohammed Matawalle tare da masu taimaka masa na musamman.
Gwamnan zai dawo Najeriya a ranar Litinin 24/06/2019.
Gwamnan zai gana da wasu daga cikin jagororin kasar Saudi Arabia Domin Tattaunawa aka yadda za a saki Dan asalin jahar Zamfara Alaramma Ibrahim Ibrahim Wanda hukumomin saudiya su ke tsare Da shi kusan shekaru biyu. Saboda tuhumarsa da su ke yi da safarar miyagun kwayoyi, da aka yi safararsu daga filin jirgin saman kasa-da-kasa na Malam Aminu Kano.
Haka zalika gwamnan zai ziyarci hadaddiyar Daular larabawa wato Dubai Domin Tattaunawa Da jagororin bankin cigaban afrika (African Development Bank) ADB tare da masu sanya hannun jari. Domin bullo Da hanyoyin bunkasa tattalin arzikin jahar Zamfara.
Kari akan hakan gwamnan zai Tattauna Da kwararru akan sha'anin tsaro a kasar Dubai Domin nemo hanyar Da za a bi Domin kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara.
YUSUF IDRIS G
Babban Daraktan Watsa Labarai Na Gidan Gwamnatin jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
16/06/2019.





