Ga dukkan alamu akwai wasu mutane da ke saka ido akan kokarin da Gwamna Matawalle ke yi a nan gida Najeriya amma su kan kauda kai daga irin wannan kokarin a waje.
Ba su san cewa tun acikin watan sha biyu (December) na shekara ta 2012 ba, kasar hadaddiyar daular larabawa (Dubai/UAE) ke daukar bakuncin Cibiyar Kasa -Da kasa da ke Yaki da Tsatstsauran Ra'ayin da Ta'addanci. Sun kau da idanuwan su a lokacin da Mai girma gwamnan jahar zamfara, Hon. (Dr). Bello Muhammad (Matawallen Maradun), ya ziyarci hukumomin tsaro, tun daga Hedikwatar Yan sanda ta Kasa da ke abuja, ya gana da shugaban Yan sanda na kasa, ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, haka zalika ya gana da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.
Har ila yau, ya ziyarci tsohon ministan tsaro, ya gana da Sarakuna,Shugabannin Fulani, Yan-sa-kai da duk masu ruwa-da-tsaki domin lalubo hanyoyin kawo karshen ayukkan ta'addanci a jahar zamfara.
Kallon kasar Dubai (UAE) a matsayin kasar da ba ta da alaka da komai na sha'anin tsaro a duniyar nan gurgun tunani ne. Kasar Dubai wuri ne da kwararru ta fannin tsaro ke haduwa domin tattauna matsalolin tsaro na duniya. Kuma Mai girma gwamnan jahar Zamfara ba abunda ya sa a gaba sai kokarin ganin ya lalubo duk hanyar da zai tsamo al'ummar jahar Zamfara daga cikin halin rashin tsaron da mu ke ciki.
Muna rokon Allah ya dafa masa ya ba shi ikon magance wannan matsalar Da ke cigaba Da kwasar rayukkan mutane a kullum!
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
18-6-2019

