GWAMNATIN ZAMFARA, TA YI NASARAR CETO YUSUF LAWAL DARE .HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 19 June 2019

GWAMNATIN ZAMFARA, TA YI NASARAR CETO YUSUF LAWAL DARE .HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE


A cigaba Da yunkurinsa na daga martabar jahar Zamfara. Tare da samar da zaman lafiya a jahar ta yadda kowa zai zauna a cikin aminci.

Mai girma gwamnan jahar Zamfara Bello Matawalle duk da yana cigaba da ibadar umara yanzu haka. Haka bai hana shi aiki tukuru ba, wajen samun nasarar ceto rayuwar Dan uwan sanannen Dan siyasar nan Dr. Dauda Lawal Dare wato Yusuf Lawal Dare.

Yusuf Dai an yi garkuwa Da shi ne watanni uku da su ka wuce baya. Wanda masu garkuwan su ka nemi sai an biya naira miliyan dari UKU (N300,000000) kudin fansa Kafin su sake shi. Sai dai bayan zamansa gwamna ta amfani Da kwararru tare kwarewar gwamnan a matsayin tsohon shugaban kwamitin tsaro da asiri na majalissar wakilai ta kasa. an yi nasarar sako shi. Talata

Gwamna matawalle ya bayar da tabbacin gwamnatinsa. Za ta tashi tsaye wajen Kare rayukka da dukiyoyin al'ummar jahar Zamfara.

     

- Ibrahim Bello Zauma
     SSA (New Media)
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here