Hakika samun sabuwar gwamnati a jihar Zamfara ya zo daidai da lokacin da matan Jahar su ke cikin wani hali na kuncin rayuwa da kuma talauci.
Sanin kowa ne gwamnatin da ta gabata ta yima Mata alkawali na kudade domin su yi sanao'i amma abin ya koma kamar an shuka dussa.
Mata suna taka muhimmiyar rawa ga kowace al'umma ta bangare daban-daban kamar bangaren siyasa, suna bada gudunmuwa wurin kokarin biyar layin zabe domin su tabbatar an samu shugaba na gari, Amma sai dai Kash! zabe na wucewa sai a manta da su.
Godiya ga Allah akan irin gwamnatin da ya bamu a yau, munga irin kamun ludayin maigirma gwamnan jaha da matar shi wurin ganin cewa an farfado da martabar jihar ta kowane fanni.
Ina Kira ga matar gwamnan jiha data taimaki mata ta samo hanyoyi domin fiddasu daga halin wahala da talauci daya addabe su. Misali gefen sanao'i, aikinyi, ilimin yara Mata, mukaman siyasa dadai sauran su.
Allah ya yi ma maigirma matar gwamna Jagora Kuma ya bata ikon bambanta jiya-da-yau.
Fatan alkhairi ga mai girma gwamna, Allah ya taimake ku ya baku ikon canza alkiblar Jahar Zamfara.

