Mai daraja gwamnan jahar Zamfara , Hon. Bello Mohammed Matawalle ya gana da jagororin ofishin jakadancin Nigeria Da ke Jidda ta Kasar Saudiya a yau Alhamis 21/6 /2019.
Inda ya Tattauna da su akan hanyoyin Da za a bi Domin sakin Dan asalin jahar Alaramma Ibrahim Ibrahim Gusau, Wanda hukumomin Kasar ke zargi Da shiga Kasar Da miyagun kwayoyi Shekaru biyu Da suka wuce.
Ibrahim Ibrahim dai Dan assalin jahar Zamfara ne.
Zaman Wanda mukaddashin jakadanan Nigeriya a kasarmu ya jagoranta wato Alh. Garba Satome Grema ya nuna farin cikinsa da ziyarar da gwamnan ya kawo a ofishin.
Haka zalika Mukaddashin jakadan ya bayyana cewa nuna damuwar da gwamnan ya yi da halin Da Malam Ibrahim Ibrahim ya KE ciki. Alama ce ta jagoranci na gari kuma abun koyi.
Grema Ya Kara Da cewa yanzu haka Wanda ake zargin yana a ofishin jakadancin a matsayin an yi belinsa. Sai dai Saboda nuna damuwar da gwamnan ya yi ba da dadewa ba za a Kai karshen wannan matsalar tare da sallamar Allaramma Ibrahim Ibrahim.
A lokacin da gwamnan ke maida jawabi. Ya yaba matuka gaya da yadda ofishin jakadancin ke fadi tashin ganin an saki Alaramma Ibrahim zuwa yau. Kari akan hakan gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta maida hankali ne, wajen yanto al'ummar jahar tare da inganta walwalar al'ummar jahar. Daga nan sai gwamnan ya nemi gudunmawa da goyon bayan ma'aikatan ofishin Domin tabbatar da an saki Wanda ake tuhumar.
Matawalle ya bayyana cewa zai tun ma'aikatar lamuran kasashen waje da ya dawo Najeriya Domin Tattaunawa akan yadda za a sako Malam Ibrahim Ibrahim, Domin ya koma cikin iyalansa.
YUSUF IDRIS G
Babban Daraktan Watsa Labarai Na Gidan Gwamnatin Jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
21/06/2019




