A lokacin da su ke jawabi Shuwagabannin fulanin daga kananan hukumomi 14 da ke jahar Zamfara. Sun bayyana cewa. Wannan ita ce ziyararsu ta farko ga sabuwar Gwamnatin jahar Zamfara, a matsayinsu na shuwagabannin Fulani, Da su ke da muhimmiyar rawar da su ke iya takawa Domin ganin an shawo kan matsalar tsaron jahar.
A Cewar shuwagabannin Fulanin ta hannun sakataren kungiyar "Mun sha tattara bayanai Da dama akan matsalar tsaron jahar Zamfara Da shawarwari Amma mun rasa wanda za mu tunkara a baya. Domin a baya mun yi zuwa wajen Gwamnatin Da ta wuce, Amma ba a ba mu damar mu bayar da bayanan da su ka dace ko saurarenmu ba a yi.
Alhamdulillahi Tunda yanzu mun samu wannan damar ta iya ganin Gwamnati. Da farko dai muna baiwa 'yan uwanmu Fulani Shawara. Da mu fito mu bayar da goyon baya ga wannan Gwamnatin Domin samun cigaban jahar Zamfara. Domin tsoronmu shi ne a baya shi ne. Da an ga kana bayar da goyon baya wajen kawo karshen matsalar za a turo a kashe ka.
"Kuma yanzu haka akwai wadanda su ka gudu Saboda tsoron kadda a kashe su. Kuma suna da muhimmanci akan matsalar tsaron jahar, Domin sun San inda matsalar take."
Da ya ke maida jawabi Mai baiwa gwamnan shawara kan sha'anin tsaro; "Gwamnatin jahar Zamfara ta yi dukkanin binciken da ya dace domin tabbatar da an samar da tsaro. Kuma Tana cigaba biyar dukkanin matakin da ya dace Domin kawo karshen matsalar.
"Wanda zuwa yanzu tana cigaba Da biyar dukkanin hanyoyin Da ya dace. Domin ganin ganin ba a cigaba Da kashe Al'umma, ba.
"Domin Al'amurra sun cakude a jahar Zamfara, Domin a baya Fulani suna Samar da nono da man shanu. Wanda ake fitar wa zuwa makwabtan jahohi. Amma yanzu an wayi gari abun ya zama tarihi.
"Dan haka ina Kira gare ku Da Duk wanda ya san yana da hannun da zai iya taimakawa Domin a samu a kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara bai yi ba wallahi sai Allah ya tambaye su.
"Dan haka a matsayin ku na shuwagabannin Fulani, dole ku tashi tsaye wajen kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara ta hanyar baiwa Gwamnatin mai-ci goyon baya.
"Hakika dole sai kun taimaka muna, wallahi tallahi yanzu, Gwamnatin jahar Zamfara a shirye take Domin kawo karshen matsalar tsaron jahar nan. Domin Matsalar ta taba kowa har ni nan kaina, ta taba ni.
"Kari akan haka mun sani cewa akwai sarakunan Da su ka Sare gandun dajin jahar Zamfara su ka baiwa manoma na makwabtan jahohi, Dan haka duk mutanen da ke amfani Da gandun dajin jahar Zamfara wajen noma, to wallahi su kwashe ina-su-inasu su bar jahar Zamfara"
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.




