Akwai wasu mabiya rosasshiyar gwamnatin Yari da su ka tashi tsaye wajen suka, Da habaice-habaice a wannan kafar. Suna fadin wai: '"Yan gwaggwarmaya sun koma biyar gwamnati dama abunda su KE bukata kenan".
Tabbas zancenku haka ne mun koma biyar gwamnati kuma abunda mu KE so ne.
Kun kwashe shekaru takwas kuna azabtar Da talakan jahar Zamfara. Wanda a farkon gwamnatinku. Mun bi ku fiye Da yadda mu KE biyar wannan Gwamnatin. Sai dai bayan kun dauki hanyar zaluntar TALAKA mu kuma mu ka fito mu ka Fara Jan hankalinku Da fada maku gaskiya. Sai dai Da yake ba wai ainahin TALAKA ne gabanku ba, sai ku ka toshe kunnuwanku daga jin koken talakan jahar Zamfara. Hakan ya cilasta muna ja baya.
Alhamdulillahi Allah ya tarwatsa bakin shirinku. Ya kawo muna Wanda ya so! Anya kuwa in muna musulman Kirki tare da yin gwaggwarmaya Dan Allah ba dole mu so shi, tare da yi masa addu'a Da fatan alheri ba?
Cikin iyawar Allah Da hawansa ya Fara dauko hanyoyin Da mu ke hasashen za su taimaka wajen tsamo jahar Zamfara daga cikin iftala'in Da ta ke ciki.
Wanda alhamdulillahi a wasu bangarorin an Fara samun nasara. To taya ba za mu so shi ba tare da Goya masa baya ba?
Dan haka kamar kullum jahar Zamfara ita ce kan gaba da komi namu. Dan haka za mu cigaba Da marawa manufofin zabin Allah.
Tare da rokon Allah ya kare shi daga Sherin mutum da aljan tare da rokon Allah ya ba shi ikon daura jahar Zamfara akan turba ta gari l c Allah duk wasu matsalolin mulki ka kare sabon gwamnan jahar Da shi. Allah ka Da ka nufe shi Da Hawan talalabiyar da ta ja Wanda ya gabace shi.
Allahumma amin.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
16-6-2019

