A cigaba da yunkurinsa na Samar da dauwamammen zaman lafiya a jahar Zamfara. Mai daraja gwamnan jahar Zamfara, Hon Dr Bello Mohammed Matawallen-Maradun ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta Samar da wuraren kiyo ga makiyaya. Wanda zai kange su ga shiga gunakkin manoma Domin Samar da zaman lafiya da fahintar juna a tsakanin manoma da a makiyaya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron jin bahasin da ya gudana ranar alhamis Da 'yan sa-kai a dakin taro na Gidan Gwamnatin jahar Zamfara.
Gwamnan ya bayyana cewa, Gwamnatinsa za ta samar Da duk wani abun more rayuwa a yankunan karkara tare da samar da tallafi ga wadanda sunka fada tarkon 'yan ta'adda. Ta hanyar fito Da shiraruwa Da za su rage radadin talauci, da ke addabar jahar baki daya.
Gwamna Matawalle ya bayyana cewa zai farfado da masakar jahar Zamfara, shirin bunkasa harkar noma wato (ZACAREB) Da kuma farfado da (ZAPA) tare kirkiro Karin hanyoyin dogaro ga kai ga matasan jahar Zamfara.
Haka zalika ya umurci a bude dukkanin karar dabbobin Da ke jahar Zamfara. Wadanda Gwamnatin Da ta shude ta Rufe, in ka debe ta Gusau, Gummi, Kasuwar-Daji da Talata-Mafara, gwamnan ya nuna rashin aminta Da rike miyagun makamai. Ya kuma bayyana duk Wanda aka ganinDa su to za a Kama shi, kuma zai fuskanci hushin hukuma daidai laifinsa.
Ya Kara Da cewa nan ba da dadewa ba. Gwamnatinsa, za ta kirkiro Da Samar da 'yan sa-kai Da su ka hada dukkanin kabilun Da ke jahar Zamfara. Domin tallafawa jami'an tsaro domin zakulo 'yan ta'adda tare da kama a maboyar su. Kari akan hakan gwamnan ya yi Kira ga 'yan sa-kai din Da kada su dauki doka a hannunsu a duk lokacin da su ka Kama bata-gari su tabbatar sun hannunta shi ga hannun hukuma Da ya dace.
Haka zalika ya shuwagabannin 'yan sa-kai din Da in sun koma garuruwansu Da su kirkiri jagorancin 'yan sa-kai tun daga matakin jaha, karamar hukuma zuwa gunduma.
Dama dai tun Ranar Talata ya fadawa shuwagabannin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria cewa gwamnatinsa za ta Samar masu makarantanni, wuraren Kiyo Domin samarwa dabbobinsu abinci.
YUSUF IDRIS G
Babban Daraktan Watsa Labarai Na Gidan Gwamnatin jahar Zamfara
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
13/06/2019
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Friday, 14 June 2019
Home
Unlabelled
GWAMNA MATAWALLE ZAI SAMAR DA WURAREN KIYO GA MAKIYAYA A ZAMFARA
GWAMNA MATAWALLE ZAI SAMAR DA WURAREN KIYO GA MAKIYAYA A ZAMFARA
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

