MURYAR TALAKA NATIONAL CONGRESS! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 17 July 2017

MURYAR TALAKA NATIONAL CONGRESS!

Muna Farin cikin gayyatar dukkannin National Exco , kwamitin amintattu na kasa da iyayen kungiyar Muryar Talaka na kasa, da kuma dukkannin states Exco. Na kungiyar Muryar Talaka. Zuwa babban taro(Congress) a birnin Gusau, Jihar Zamfara ranar Juma’a, 4-8-2017.


Dukkanin Wadannan da aka gayyata za su iso Gusau Ranar Jumma’a, 4/8/2017.

Za a hallara dakin taro da misalin karfe 8:30 Pm, sannan za a tantance dukkanin wakilai, a fara taro da misalin karfe 9:30Pm a kamala a daren Insha Allah.


Ana bukatar shugabannin jihohi (Chairmen) su turo da sunayen State Exco. Ko wadanda za su wakilce su Zuwa ga National Secretary General Comrade Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina daga yau zuwa ranar 30-7-2017.

GARGADI: Ba za a bar duk wanda ba a gayyata ba, shiga dakin taron.  Haka zalika, duk wanda bai cikin wadanda aka gayyata ba zai shiga dakin taro ba.


Daga karshe muna yima dukkanin membobinmu fatan alheri, tare da fatan Allah ya kawo su Gusau lafiya, mu yi taro lafiya, kowa ya koma gida lafiya.



 SANARWA: COMRADE UMAR GIDADO GUMMI NATIONAL P.R.O.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here