Al'ummar Najeriya na cike da murnar dawowar shugaba Buhari, bayan da ya kwashe kwanaki 103 yana jinya a kasar Burtaniya.
Idan dai za ku iya tunawa ranar 19 ga watan Janware ne shugaba Buhari ya fara fita kasar Birtaniya domin
"hutun jinya" haka a ranar 7 ga watan Mayu - Ya sake komawa Birtaniya dan duba lafiyarsa.
Dirar jiginsa dake dauke da Shugaba Buhari ke da wuya, yasa babban Birnin tarayya ya cika ya batse, inda ya samu tarbar Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ministoci da jami'an tsaro da sauran jiga-jigan gwamnati, gwamnoni, 'yan majalisu, manya-manyan 'yan siyasa da talakawan da suka yiwa Abuja cikar kwari.

