SHIRUN DA JAGORORIN JAHAR ZAMFARA SU KE CIGABA DA YI AKAN MAGANAR MASU HANNU GA WALAKANTAR DA ALKUR'ANI YANA SANYA ALAMOMIN TAMBAYA GA MU MUSULMAN JAHAR
Kusan Shekaru biyu da fara ganin wasu tsinannu na walakantar da alkur'ani Mai Girma, ta hanyar yayaga shi tare da sanya shi cikin masai/shadda/salga ko In ce bandaki.
In ka debe rokon Allah ya tona asirin masu wannan aika-aikar, tare rokon Allah ya walakantar da masu yi, to ban taba cewa Kala ba.
Sai dai Akwai wasu abubuwan na tusgo Wanda dole in mu ce wani abu domin Sauke nauyi. Musamman ganin yadda ake kokarin mantawa da abun duk da girman tasirinsa.
Da farko dai alkur'ani na daya da littafai hudu da Allah ya saukarwa manzanninsa. Domin ya zama abun biya ga al'ummar annabawan.
Alkur'ani shi ne anka saukarwa Annabi Muhammadu (S. A. W).
A tarihin duniya kaf! Ba a taba wani littafi da ya ko kusa da darajjar Alkur'ani ba. Haka zalika ba a taba wani littafi Mai tsarki,martaba, mu'ujiza, da darajja irin ta alkur'ani ba.
Abun mamakinmu shi ne, tun da anka saukar da wannan littafin. Ko Wanda yafi kowa kafurci, a duniya ba mu ji ya walankata alkur'ani kamar yadda, wasu daga cikin wawayenmu sunka yi a jahar Zamfara ba.
Wanda a lokacin da munka fara ganin hotonan alkur'anai a cikin masai/shadda hakalinmu ya tashi matuka. Inda munka yi ta roke-roken Allah ya tona asirin masu wannan aika-aikar.
Kuma mun yi mamaki matuka wai a jahar Da ke da kima a idon duniya ta fuskar addinin musulunci ne. Za a wayi gari Anna walankata Babban littafin da ke koyar da addinin a haka. Wanda a lokacin mun ta sake-sake Anya kuwa ba wai wasunmu ne, ke yi muna wannan aika-aikar ba.
Kwatsam! Allah maji rokon bayinsa ya amshi addu'armu ta hanyar tona asirin masu wannan aika-aikar. Wanda abun mamaki shi Wanda anka Kama din cikinmu ya ke.
Wanda tuni yana hannun jami'an tsaro suna bincikarsa.
Sai dai abunda ya tayar muna da hankali shi ne; yadda anka yi Wata da watanni har yanzu ba mu ji wani labarin yadda ake ciki akan wannan badakalar ba. Wanda har mun fara jin wai ya dauki lauya duk da tun farko ya bayyana shi ne, ke aika-aikar tare da bayyana wasunsa da ke da hannu dumu-dumu (duk da daga baya an wanke su)
Ya kamata mu sani;
Shin wane boka ne, ke sanya shi wannan aika-aikar?
Suwa ne ne ke sanya shi?
Da Wace manufar su ke wannan aika-aikar?
Domin na tabbatar Wanda anka Kama dumu-dumu da hannu a wannan aikin, ba shi ke sanya kansa ba. In har shi ke sanya kansa to yana da masu tallafa masa. Kuma Akwai wasunsa da su ke aikata wannan mummunan aikin.
Babban abun bakin ciki Wanda ba za mu manta ba a lokacin da anka fara wannan aika-aikar ne Allah ya yiwa Marigayi Ummaru Shinkafi rasuwa, Wanda Kai tsaye gwamnatin jahar Zamfara ta maida hankali kan juyayi na rashinsa. Kwata-kwata anka manta da an taba alkur'ani.
Babban abunda ya kamata mu Lura shi ne; mu musulmi ne, mun yarda da kaddara ce ta fadawa al'ummar MAIDUGURI dama al'ummar arewa maso gabas, na mummunan kashe-kashe na boko Haram. Amma da dama daga cikinmu na hasashen isgilancin da al'ummar yankin sunka ta yiwa alkur'ani ne, a Shekarun baya ya sa Allah ya jefa su cikin wannan kuncin na tashe-tashen hankulan.
Wanda muddun ba, tubarwa Allah, ta hanyar hukuncinsa akan masu walakantar da littafinsa ba, to wallahi ina tausayawa Allah ya jiyu da hushinsa gare mu.
Dan haka muna Kira ga gwamnatin jahar, gwamnatin wadda takenta shi ne; ADDININMU-AL'UMMARMU. Haka zalika Babban inkiyar jahar Zamfara ita ce, shari'ar musulunci.
Da su tashi tsaye dan tabbatar da cewa; duk wani Wanda anka Kama da laifi a wannan badakalar, a tabbatar an hukunta shi, hukunci akan shari'ar musulunci. Domin wallahi hakan kawai za ku yi ya tserar da al'ummarmu da addinin namu. Daga fadawa daga cikin fushin Allah.
Daga Karshe muna rokon Allah ya baku ikon zartar da hukuncin da ya dace kan wadannan mushiriki da waka-junansa. Duk wani Mai hannu a wannan badakalar, ya Allah duk wani abu da ya ke takama da shi, ka fi shi, shi. Assalima Kai ka ba shi, shi.
Ya Allah ka kwace abunka, daga Karshe ka walakantar da rayuwarsa fiye da yadda ya walakantar da littafinka da ka yi alkawarin karewa.
Ya Allah kada ka Kama mu da laifin da wasu daga cikin wawayenmu sunka yi maka.
Allahumma amin.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Matasan Zamfara Ta Tsakkiya)
08069807496
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Sunday, 7 January 2018
Home
Unlabelled
SHIRUN DA JAGORORIN JAHAR ZAMFARA SU KE CIGABA DA YI AKAN MAGANAR MASU HANNU GA WALAKANTAR DA ALKUR'ANI YANA SANYA ALAMOMIN TAMBAYA GA MU MUSULMAN JAHAR
SHIRUN DA JAGORORIN JAHAR ZAMFARA SU KE CIGABA DA YI AKAN MAGANAR MASU HANNU GA WALAKANTAR DA ALKUR'ANI YANA SANYA ALAMOMIN TAMBAYA GA MU MUSULMAN JAHAR
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.
