A jiya Lahadi 6-5-2018 ta gana da Hon. Sagir Hamida. Ganawar Wadda ta gudana a jahar Kaduna.
Da Fara ganawar jagororin kungiyar na jahar Zamfara suka Gabatar da Kansu ga mai masaukin baki. Daga nan aka Gayyato Shugaban tafiyar wato Ambasada Nura Isah Gusau Wanda ya fede biri har wutsiya Akan manufar kungiyar da kudurorinta.
Da ya ke maida Jawabi Hon. Hamida, Hakika Kun yi matukar dabara da kunka hada tarin Matasa masu ilimi da kishi a cikin wannan tafiyar. Dan haka A matsayina da ke son cigaban Matasa, da kuma sanin matsalolin da al'ummar jahar Zamfara mu ke fuskanta. Zan iya wayina na Mara maku baya.
Hakika Kuna kan hanya Mai kyau. Domin tun a zamana na siyasa ban taba haduwa da wata kungiya mai Matasa wadanda sunka yi Karatu, Kuma su ka tsarawa kansu yadda za su taimaki al'umma irinku ba.
Daga nan ya shawarci 'ya'yan kungiya kamar haka;
Akwai bukatar ku rungumi Fadakar da al'ummar jahar Zamfara akan yadda ya dace su gudanar da al'amurransu na yau da kullum. Domin sai da fadakarwar NE, za a samu cigaba mai Dorewa. Sai kuma Koyawa Matasa hanyoyin dogara da Kai, da Kishin jahar zamfara tare da kokarin Sanya jahar gaba a Dukkanin al'amurranku. Tare nemi shuwagabanni na gari ta hanyar zabar mutane na gari domin jagorancin al'umma jahar.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau SSA ON MEDIA AND PUBLICITY LABOUR ROOM GLOBAL INITIATIVE.


