Yanzu haka suna hannu 'yan sanda Husaini Ibrahim Walin Magami taubashi na ne da innata da mahaifinsa uwa daya uba daya su ke,
yana Sana'ar sayar da wayoyi ne sabbi a garin Magamin mai Tarko ya ke da ke nan cikin karamar Hukumar Gusau!
Kasa da awa daya da rabi ya kirani ba Ni jinsa ya sake kirana na. Ya ce; "Abdulmalik ga ni cikin garin Gusau, Abokina Commarade Babangida Bukari gayyato ni wajen wani taro"
Na tambaye shi wane taro?
Ya ce; "Wallahi kawai ya cilasta Mani NE, domin Abokina NE, Kadda ya ga kamar ban son cigabansa, Taron MARAFA (Sanata mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, kuma Dan Takarar gwamna a jam'iyar APC) ne, har an yi Mani EXCO na jam'iya. Ya Kake gani ba matsala"?
Kai tsaye na ce masa, kash! Husaini Allah ya rufa maka asiri bakin gwargwado kana cikin wadata Kar ka jefa kanka cikin wani mummun hali na banza.
Domin ina hasashen abunda zai faru shi ne, za a raba APC biyu ne, domin nasan dai zaben EXCO na WARD na APC an yi shi Tun makon da ya shude!
Dan haka wallahi karka yarda ka jefa kanka a Siyasar banza, ko shi Wanda ka biyo din ba ni tunanen wanda ku ke yi kansa zai yi tasa. Dan haka ina baka shawarar ka ja baya ka cigaba da kasuwancinka.
Ya ce; "to ya yi daidai nagode, dama shi ya sa na kiraka ka ba Ni shawararwari Dan ban san yadda abun ya ke ba"
Kwatsam! Ban yi minti ashirin da kwantawa ba, Sai ga wayarsa ta yi Kara, kafin a miko mini ita ta yanke. Na kira ba a dauka ba, ko da na Duba Sai na ga Ashe ma wannan shi ne kira na biyu da ya yi mini Duk ban ji ba. Na ga Message har uku kamar haka;
1- "Abdul wlh yan ctu (Yan Sanda) sun Kama mu yanxu haka"
2- "Muna tudun wada"
3- " Unguwar Gwaza head queter"
Ina ganin wannan sakonni hankalina ya tashi!
Domin sakon farko ya turo mini shi 11:20am na karshe Kuma 11:26am.
Yanzu da na ke wannan rubutun number dinsa na ke kira ba a dagawa. Wanda hakan ke tabbatar mini da cewa, jami'an Tsaron sun karbe wayoyinsu!
Wannan ita ake Kira bakar Kaddara,
Domin Duk duniyar nan ba Ni tunanen yana da wani da ya kamata ya San da wannan matsalar kuma ya yi wani Abu akai kamar Ni! Sai dai kuma Ni Kai yanzu ban San ta inda zan Fara fuskantar wannan matsalar ba. Domin dai matsalar ta siyasa ce kuma na tabbatar Daga sama take!
Dan haka zan Fara da kira ga su wadanda sunka tara su, da su yi Duk mai yuyuwa wajen fitar da su cikin wannan halin da sunka jefa, Wanda na tabbatar hakan zai Kara masu kwarjini gare su, in Kuma sunka zura masu Ido, abunda na zarga zai tabbata.
Cc;
Kabiru Garba Marafa
Mai'aya Tsafe
Maikatako
Shamsu Kasida
Kafilu Abdullahi Gusau
Nafiu Rufa'i Imam
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
12-5-2018
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Saturday, 12 May 2018
Home
Unlabelled
SIYASA MUGUWAR WASA.... YAN SANDA(police) SUN KAME SU YANZU HAKA, DOMIN SUN ZO TARON APC A BANGAREN SANATA MARAFA
SIYASA MUGUWAR WASA.... YAN SANDA(police) SUN KAME SU YANZU HAKA, DOMIN SUN ZO TARON APC A BANGAREN SANATA MARAFA
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

