Wata kungiya mai fafutukar tallafawa wadanda iftala'i ya shafa tallafawa 'Yan gudun hijira Maza da mata Yara da mata tsoffi ke zaune da wani yanki na Damba a cikin garin Gusau.
'Yan gudun hijirar da da yawansu ya Kai 300 da suka fito Daga karamar Hukumar mulkin Bungudu, akalla sun shafe sama da Shekaru uku suna gudun hijira a cikin unguwar Damba.
A zantawarmu da su, lokacin da kungiyar Victims Of Violence Charity Foundation ta kawo masu tallafi, sun tabbatar muna da cewa, in ka Debe wannan kungiya da ta kawo masu dauki a shekarar da ta wuce, yau sama da shekaru uku su ke gudun hijira a wannan wuri, amma Gwamnati ko wata kungiya bata taba kawo masu dauki ba, Duk da fama da rashin Lafiya, abinci da rashin matsugunnin da su ke fama da shi.
Kungiyar tallafa masu da Suturu, Magani, abinci da kuma ba su shawarwarin da kwararrin likitocin da kungiyar take da su suka yi









