MATAIMAKIN GWAMNAN JAHAR ZAMFARA YA RABA SUTURUN SALLAH DUBU GOMA SHA DAYA (11,000) GA GAJIYAYYU DA MARAYU! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 4 June 2018

MATAIMAKIN GWAMNAN JAHAR ZAMFARA YA RABA SUTURUN SALLAH DUBU GOMA SHA DAYA (11,000) GA GAJIYAYYU DA MARAYU!


A yunkurinsa na ba da tashi gudunmawa ga masu Dan karamin karfi da marar Galihu. Mataimakin gwamnan jahar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman.

Ya yi rabon turame ga mata 5000 masu Dan karamin karfi tare da baiwa, Maza masu karamin karfi 5000 Shaddodi domin samu suturar da za su yi bikin Sallah da ita. 


Haka zalika Sarkin Malaman ya baiwa Yara Marayu Maza da mata dangin Shaddodi da turame har dubu 717.

Da ya ke jawabi a wajen bada Tallafin Marayun, da ya gudana  a yau Litinin 4-6-2017, a harabar gidansa da ke albarkawa Gusau, Mai Daraja Mataimakin Gwamnan Jahar Zamfara ya bayyana cewa; "hakika al'umma na cikin bukatar tallafi a daidai wannan lokaci shi ya sa muka ga ya dace, mu Kara fadada wannan aikin da mu ke yi na tallafawa wadannan Yara Marayu, makwabta da za su samu suturar da za su yi bikin Sallah da ita. Dan haka muna kira ga sauran al'umma da su dukufa wajen taimakon masu Dan karamin karfi, domin saukaka, masu tare da faranta masu rai a lokacin bukukuwan Sallah.


An dai baiwa Marayun Shaddodi da turame tare da Naira dubu-dubu kowanensu domin dunke suturar da aka ba shi.




Post Bottom Ad

Responsive Ads Here