Wata kotun Shari'ar Musulunci da ke zama a Gusau. Ta yankewa tsohon Shugaban Jam'iyar APC NA mazabar Sabon gari. Da wani mutun daya hukuncin KISA ta hanyar Datse Kansu da Takobi har su mutu.
Akan laifin da aka Kama su da shi na sanya yara biyu suna jefa AL'KUR'ANI Mai Tsalki a cikin Masai. Inda shi kuma yaro daya daga cikin yara biyu dinda aka Kama, aka bayar da umurnin Kai shi gidan marayu na zaman Shekara da uku da damar in ya tuba za a sake Bayan Shekaru ukun in kuma bai tuba ba za a Kai shi gidan Yari.
Haka zalika kotun Ta Wanke Shugaban Karamar hukumar Gusau da Kansilan Gundumar Sabon gari Gusau. Saboda ba a samu shedun da za su tabbatar da cewar su ke sanya wadanda ke jefa AL'KUR'ANI Masai din su ke sanya su ba.
Sai dai kotun ta baiwa wadanda aka samu da laifi damar daukaka Kara nan da wata daya (30)
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. Daga harabar kotun da ke nan Unguwar Yarima Gusau

