BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA SHUGABA BUHARI DA MANYAN AREWA MASO YAMMA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 6 May 2019

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA SHUGABA BUHARI DA MANYAN AREWA MASO YAMMA!



Tare da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya a daidai wannan lokacin, na zabi rubuto maku wannan wasiƙa a daidai wannan lokaci domin yi maku hannunka mai sanda tare da farkar da ku daga mummunan barci da ke dab da illata ku dama al'ummarku baki faya.

Da farko zan fara da Shugaba Muhammadu Buhari da tsatsonsa ya ke a wannan yankin da ke zama mafi yawan al'ummar Najeriya dama jahohi mafi yawa har guda bakwai.

Mai girma Shugaban ƙasa, zan ɗan yi maka wani tuni. Kai ne mutum ɗaya tilo a tarihin dimukaradiyar Najeriya wanda ya ci zaɓe a ƙarƙashin tutar jam'iyar adawa tare da kayar da Shugaban kasa mai ci, ba kuma tare da an sayi al'umma da kuɗaɗe ba. Wanda a tarihin Najeriya ba a taɓa yin ko kusa ga hakan ba. Kuma tsantsar ƙaunarka da mu talakawan Najeriya ke yi ne ya sa mu ka zaɓe ka, saboda aminci da yarda da mu ke da shi akanka. Wanda mu ke tunanen za ka iya tsamo ƙasarmu daga baƙin taɓon da ta faɗa har ya hana ta yin gaba. Hakan ya sa duk kuɗin da Gwamnatin da ka kayar ta baiwa Talaka bai yi tasiri wajen kawar da ita kan mulki ba. Domin babban gurinmu a lokacin shi ne samun shugaba adili da zai tsame ƙasarmu daga taɓon da ya hana ta ci gaba.

Babban abunda ya sa mu ka Ƙi Gwamnatin Goodluck Jonathan a lokacin har mu ka jefar da shi kwandon shara bai wuce matsalar rashin tsaron da ta adabi yankin arewa maso Gabas dama mafi yawan jahohin arewa ba, wanda a lokacin Boko Haram ta yi wa Mummunar barna. Wanda sakaci na Gwamnatin ya sa kullum 'yan Boko Haram su ke cin karensu babu babbaka tare da ƙara faɗaɗa ayukkansu, na ta'addanci a doron ƙasa.

Ganin kai masani tsaro ne, da ka yi aikin soji har ka kai Janar ya ƙara muna ƙarfin guiwa wajen zaɓenka domin muna da tabbacin kasan ƙauli da ba'adin matsalar tsaron kasarmu ba wai yankin arewa kurrum ba.

Alhamdulillahi mun zaɓeka kuma ka yi ƙoƙarin cin galabar Boko Haram da kaso mai girma. Domin an ci nasara akansu matuƙar gaske, tare da ƙwace dukkan ƙananan hukumomin da su ke da iko da su a baya. Tare tsayar ds faɗaɗa aikin ta'addancinta. Tabbas mu al'ummar Arewa da Najeriya mun yaba da hakan, kuma Muna cigaba da alfahari da haka.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, Mai girma Shugaban kasa, a yau an wayi gari Yankinka ya faɗa cikin irin wancen mummunan halin matsalar tsaron. Wanda da farko abun yana faruwa ne kurrum a jahata ta zamfara, wanda har yanzu nan ya fi muni. Wanda mu mazauna zamfara mun san akwai sakaci ɗari-bisa-ɗarina gwamnanmu akan cigaba da kashe-kashen da ake yi muna. Wanda a baya matsalar ko a jahar Zamfara da abun bai wuce wasu 'yankuna na Maru a Ɗansadau, da 'Yargaladima da ƙaramar hukumar Tsafe a ƙauyen Kizara ba sannu-sannu abun ya yi faɗaɗa, har aka wayi gari mummunan rashin tsaron ya mamaye Zamfara baki ɗaya kullum cikin zubar da jini ake yi. Rayuwar Ɗan Adam ta zama kamar ta kiyashi fyaɗe, da satar mutane da ƙone dukiyar al'umma ta zama ƙawa a duk faɗin jahar baki ɗaya. Sannu-sannu ya shiga maƙwabtan jahohin Sokoto da Jaharka ta katsina da shi kansa garinka na Daura da ko makon jiya an sace surukin dogarinka. Haka zalika in mu ka duba sannu-sannu matsalar ta karaɗe kusan dukkanin jahohin yankin Guda bakwai. Kuma kullum matsalar ƙaruwa take yi musamman a jahohin Zamfara, Kaduna, katsina da kuma Sokoto da Niger da kuma Jigawa a Kano ɗai ne abun ke da dama-dama Wanda ko su abun ya yi masifar taɓa su domin hanyar zuwa jahar ta zama tarkon mutuwa ga Zamfarawa da Katsinawa, Sakkwatawa da Kabawa.

Mai girma Shugaban kasa kaɗan kenan daga cikin matsalar tsaron da ke fuskantar yankinka.

Haƙiƙa shugaba Buhari wannan yanki na buƙatar gudunmawarka ɗari-bisa-dari,  domin har yanzu ainahin matsalar tsaron yankin ba a ɗauko hanyar magance ta kamar yadda ya dace ba. Domin jami'an tsaron da ke iya tsayar da matsalar sun ƙaranta da kayan aikinsu matuƙar gaske, Wanda ko a ranar 5-5-2019 Sarkin Kudun Ɗansadau ya shedawa duniya a shirin safe da hantsi na BBC HAUSA cewa kashi sittin cikin ɗari na matsalar tsaron Zamfara a Masarautar Ɗansadau ta ke Amma har yanzu ba a kawo masu jami'an tsaron da za su fuskanci matsalar ba.

Haka zalika akwai wasu matakai da aka ɗauka wanda alhamdulillahi ɗayan zai taimaka mauƙar gaske, Wato hana haƙar ma'adanai a jahar Zamfara da nan ne cibiyar tashin hankalin arewa baki ɗaya, to Amma Wallahi matakin da Gwamnatin jahar Zamfara ta ɗauka na taƙaita yawo da babura a wani lokaci wanda yanzu har ya kai an haɗa da babura masu ƙafa uku-uku (KEKE NAPEP) haƙiƙa wannan matakin yana taimakawa ne kurrum wajen ƙara janyo masifa ga al'ummar jahar. Domin masifaffen rashin aikin yi ya ƙaru. Ga masu neman abinci da babura tare jefa al'ummar da ba su ji ba su gani ba cikin masifo kwatsam na ji a BBC HAUSA cewa an Haramta yawo da babura a wasu jahohin yankin (wannan maudu'i ne mai zaman kansa da za mu yi magana akansa gaba).

Mai girma Shugaban ƙasa, bala'in da mu al'ummarka mu ke ciki wallahi yana buƙatarka kacokan! Kuma wallahi muddun ka yi wasa sai wannan matsalar ta zarce ta Boko Haram a Najeriya baki ɗaya. Kuma dole a ɗauki matakan samawa matasa makoma ta gari ba wai Ƙara jefasu cikin masifo da a ke yi yanzu ba.

Haka zalika ku kanku Jagororin wannan yankin wallahi kuna da babban Aiki a gaba gare ku. Domin kun yi shiru ana kisan al'ummarku duk wata gudunmawa da za ku iya bayarwa kun ƙi a zahirance. Ƙila kuna taƙamar kuna da dukiyar da za ku iya ɗaukar hayar jirgi ya kwashe maku shirginku ko? Lalle in hakan ne to wallahi kunyi raggon tunane. Domin ba ku da Inda ya fi maku wannan yankin, nan Allah ya halicce ku, nan za ku zauna ku ji daɗi kowace duniya kuka je za ku buƙaci dawowa gida cikin al'ummarku.

Dan haka ya zama dole gare ku, ku kanku ku tashi tsaye ku bayar da taku gudunmawa tun daga ta taimakawa a yaƙi talauci da rashin aikin yi da ya yi wa yankinku katutu har ya taimaka wajen samuwar ƙungiyoyin ta'addanci da kuma taimakawa da Shawarwari da ma matsin Lamba ga shugaba Buhari da ya Kalli al'ummarsa. Kamar yadda na wasu yankuna ke yi. Wanda ni ina ganin yanzu akwai buƙatar yin wata ma'aikata da za ta kula da kuma farfaɗo da yankin Arewa maso Yamma kamar yadda ake da ta Niger-delta da Arewa maso Gabas. Domin ta Kula da na farko dai abun ya kawo tada zaune tsaye a wannan yankin hanyoyin da suka  dace a bi domin magance matsalolin. Da kuma ƙoƙarin sake fasali da ƙara gina yankin baki ɗaya, domin ni dai Wallahi na san yanzu kashi arba'in na mutanen zamfara yanzu sun tarwatse musamman na karkara. Da ake kisa kullum.

Wanda muddun aka yi haka to da ikon Allah zaman lafiya zai samu a yankinmu, kuma cigaba za zo insha Allahu.

Daga ƙarshe muna rokon Allah ya ɗaukaki wannan yanki namu, arewa, ƙasarmu Najeriya. Ya kawo Muna zaman lafiya mai ɗorewa ya, ba mu shuwagabanni nagari.

Muna roƙonka Allah ya sa wannan koken namu ya kai ga waɗanda mu ka yi domin su ya kuma ba su ikon share Muna hawayenmu. Allahumma amin.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau ( Jami'in Hulɗa Da Jama'a Na Ƙungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

6-5-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here