SANATA NASIHA, YA JIƘE AL'UMMARSA DA RUWAN ALHERAI! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 10 September 2019

SANATA NASIHA, YA JIƘE AL'UMMARSA DA RUWAN ALHERAI!











Domin tallafawa Jin daɗi da walwalar al'ummar da ya ke wakilta. Sanata Hassan Muhammad Nasiha Gusau, yau ya jiƙe al'ummarsa da Ruwan alherai. Wanda ya yau Sanatan ya ƙaddamar a filin wasa na Sardauna Memorial Stadium Gusau. Inda Sanatan ya ƙaddamar da rabon kayan Tallafi ga al'ummarsa

Da ya ke Jawabi a wajen ƙaddamar da bayar da gudunmawar ya zayyano wasu ayukkan alheri da ya yi lokacin da ya yi Sanata a shekaru 8 baya. Daga nan ya ƙaddamar da bayar da waɗannan kaya kamar haka: Motoci guda 18 ƙirar 406 guda 6 Mercedes guda 11 sai Bos 1, Firjin 18, babura 21, Littafan  addini kwali 18, injinan Markaɗe 45, atamfofi buhu takwas. Da sauransu.

Haka zalika Sanatan ya ƙara da cewa za su cigaba da aiki tuƙuru domin inganta rayuwar Al'umma ta hanyar inganta rayuwarsu. Musamman tabbatar da cewa dukkanin ma'aikatun Gwamnatin Tarayya sun shigo jahar Zamfara domin tallafawa jahar. Tare da inganta Sha'anin Ruwan sha da ilimi ta hanyar inganta makarantannin FUG da FCET GUSAU.


Da ya ke Jawabi a wajen ƙaddamar da bayar da waɗannan kaya, Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya nuna matuƙar jin daɗinsa ga yadda ya ga wannan Sanatan ya yunƙuro domin tallafawa waɗanda su ka wahala da shi.


Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatinsa Tunda ta yi nasarar Samar da tsaro a jahar Zamfara dan haka za ta mayar da hankali wajen inganta Rayuwar al'umma. Saboda haka ne ya sa Gwamnatinsa ta bayar da umurnin ƙarawa Malaman Firamare 6709 girma. Ƙari akan Hakan gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatinsa ba za ta yi yawance-yawancen banza ba. A madadin haka zai mayar da hankali wajen yin ayukkan da za su inganta rayuwar Al'umma a duk Inda ya samu kansa. Daga ƙarshe ya nemi al'ummar jahar Zamfara da su cigaba da Sanya Gwamnatinsa a cikin addu'o'insu na yau da kullum. Domin a cewarsa addu'ar su ce ƙara ɗora Gwamnatinsa kan tafarkin tallafawa al'ummarsa kamar yadda ya fara.

Taron dai ya samu halartar Sakataren Gwamnatin jahar Zamfara Hon. Bala Bello Maru, Sarkin Katsinan Gusau, shugaban jam'iyar PDP na jahar Zamfara. Alh. Ibrahim Mallaha Gusau. Da sauran Muhimman jama'a.


 Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

10-9-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here