MA'AIKATAR LAMURRAN ADDINI TA ZAMFARA, TA KARYATA LABARIN CEWA ZA TA KASHE NAIRA BILIYAN 1 GA MASALLATAI DA MAKABARTUN JAHAR. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 2 January 2020

MA'AIKATAR LAMURRAN ADDINI TA ZAMFARA, TA KARYATA LABARIN CEWA ZA TA KASHE NAIRA BILIYAN 1 GA MASALLATAI DA MAKABARTUN JAHAR.

A cikin wannan makon ne, labari ya yi ta yawo a kafafen Sada zumunta cewa "ma'aikatar Lamurran Addini ta jahar Zamfara ta ware Naira biliyan daya domin gyara masallatai a jahar da kuma makabartun jahar" labarin da ya yi ta yawo kamar wutar daji.

Sai dai Kwamishinan Ma'aikatar Lamurran Addini na jahar Zamfara Liman (Dr.) Muhammadu Tukur Sani Jangebe, ya bayyana cewa wannan labari kwata-kwata bai da tushe balantana makama.

Da ya ke bayyani ga manema Labarai Kwamishinan ya bayyana cewa masu yada Wannnan labarin makiya Cigaban jahar Zamfara ne, domin ba wani labari mai sunan an debe wadannan kudaden. Hasalima dai Ma'aikatar lamuran Addini ta gabatar da kasafin kudin da ta ke son majalissar ta aminta domin yin ayukka a hukumomi kamar haka:

1- Zakat and Endowment Board 
2- Preaching Board 
3- Directorate Of Quranic Welfare 
4- Shari'ah Research Commission 
Da ita kanta dukan ayukkan da ma'aikatar Lamurran Addini za ta yi din na 2020. Wanda ya shafi duk wani Abu da ya shafi Cigaban Addini da daukaka shi. Wanda zuwa yanzu ita Majalissar ba ta ma kammala sauraren ma'aikatu ba,  balantana a yi Maganar Gwamna ya ware wasu makuddan kudade domin aiki biyu kurrum har biliyan daya.

Daga nan ya yi kira ga masu Watsa wannan jita-jita da su ji tsoron Allah su dena, domin zunzurutun karya ce kurrum.

Abdulmalik Saidu Maibiredi 
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
2nd January 2020

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here