A cigaba yunkurinsa na ganin ya bi umurnin Mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun na umurnin duk Mukarabansa su tashi tsaye domin tallafawa Al'umma. Don yakar talaucin da Al'ummar jahar Zamfara ke fama da shi.
Kwamishinan tsaro da ayukkan cikin gidan jahar Zamfara, Hon. Abubakar Justice Dauran ya kaddamar da tallafa masu Dan karamin karfi har 600 a Mazabarsa ta Dauran da ke karamar hukumar Zurmi a jahar Zamfara. Abubuwan da aka raba sun hada da suturu ga maza da mata da kuma kungiyar Fulani da shuwagabannin Jam'iyar PDP ta gundumar. Tare da malaman Addini da kuma limamai da su ka amfana da kuma Alkur'anai masu girma ga dukkanin makarantannin addinin musulunci da ke gundumar. Da kuma kudade.
Da ya ke jawabi Kwamishinan tsaron ya bayyana cewa ya yi wannan shirin ne, domin tallafawa masu Dan karamin Karfi Kamar yadda mai girma Gwamna ya umurce mu da mu yi.
Haka Zalika Kwamishinan ya bayyana cewa zai yi irin wannan shirin a dukkanin Yankuna uku na karamar hukumar Zurmi da wasu yankuna na jahar Zamfara, domin tabbatar da Al'umma sun samu saukin rayuwa. Kari akan hakan Kwamishinan ya yi amfani da wannan damar Inda ya yi kira ga 'yan uwa fulani da su cigaba da zaman lafiya tsakaninsu da Hausawa.
Da ya ke jawabi a madadin mai Daraja Gwamnan jahar Zamfara, Tsohon kantoman Soji na jahar Nasarawa Kanal Bala Mande (mai Ritaya) ya yi jinjina ga wannan Kwamishinan, tare da shawartarsa da ya rike wannan kyakkyawan aiki domin tallafawa Al'umma. Haka Zalika ya shawarci sauran 'Yan siyasa da su yi koyi da wannan dan tahaliki.
Bikin raba kayan dai ya samu halartar manyan Yan siyasar karamar hukumar Zurmi Malamai, uwayenmu mata da matasa da sauran Al'umma.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
8-2-2020
8-2-2020

