BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNA ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI NA JAHAR ZAMFARA. AKAN NUNA HALIN KO IN-KULA DA MARAYUN JAHAR.
Tare da fatan kana cikin koshin Lafiya, ya mai Girma Gwamnan Gwamnonin Najeriya. Tare da fatan komi na cigaba da tafiya kamar yadda ya dace! Allah ya sa haka.
Ya mai Girma Gwamna kacokan yau na Doro Alkalamina Karo na farko domin rubuta maka wannan wasika. Kan balahirar da kusan ita ce ta dauki hankalin 'yan uwa Zamfara a mako daya zuwa biyu da sunka shude. Wato halin da Marayun da Ke zaune a gidan Marayu daya tilo dake jahar Zamfara ya Ke ciki.
Inda anka ruwaito wata hira da anka nado wani Bawan Allah na kokarin shedawa wani hadiminka, halin da marayun su ke ciki. Domin ya sanar da kai, Kai kuma ka dauki matakin kawo wa Wadannan bayun Allah dauki. Wanda a cikin sakon muryar ake mika wasu sakonnin halin da su Marayun ke ciki. Tun daga barinsu da yunwa, salwantar da su, Hana masu damar yin karatu yin karatun kamar yadda ya dace, kwashe duk wani taimako da wani ya kawo gidan da sauran korafe-korafe matara Kama da haka. Da ake yiwa Kwamishiniyar mata da kananan yara ta jahar Zamfara wato Hajiya Balkisu Ibrahim Ahmad Bundugu da yi.
Wanda Bayan fitar wannan sakon murya ne, sakon ya jawo hankalin Al'ummar jahar Zamfara da Kungiyoyin kare hakkin mata da kananan yara da mata na jahar Zamfara, 'yan Jaridu da lauyoyi sunka yi caa! A gidan Marayun da zummar tabbatar da wannan zargi da ake yiwa wannan Kwamishiniyar.
Wanda kungiyar muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara na daga cikin kungiyoyin da sunka kai hawa, a wannan gidan Marayun. Duk da kafin zuwan kungiyar kwamishiniyar ta yi duk mai yuyuwa dan tabbatar da cewa Marayun ba su gana da wasu 'yan jaridu ko wata kungiyar ba. Kamar yadda na ganewa idaniyata Bayan Kwamishiniyar ta sa a kwashe, masu Wayo a cikin marayun inda na yi nasarar yin hira da marayu uku daya da ya samu rauni a kokarin tserewa yunkurin Kwamishiniyar da kuma daya da kwamishiniyar ta Kora daga gidan da kuma wani yaro da bai kai Shekaru sha 13 da ya tabbatar shi Ne Kwamishiniyar ta Mammara bayan mai Girma Gwamna ya ba shi naira dubu goma ta zo karba ya taba naira dubu da zummar sayen takalmi, a cewarsa.
Babban abunda Zai ba mu tabbacin Cewa Akwai wani mummunan hali da marayun su Ke ciki, wato yadda kwamishiniyar Ta ke cigaba da yin tubka da warwara. Inda ta ke kokarin karyata zargin da ake yi mata na jefa Marayun cikin halin kaka-nika-yi. Hujja a nan ita ce, ranar 5-7-2017 na Jagoranci hira kai tsaye da ita Kwamishiniyar a ofishinta da Ke Gusau. Kai Tsaye bayan hirar ta kankama duniya na ji da Saurare. Anka umurci kwamishiniyar da ta yi gaugawar dena hira da mu Kai Tsaye. Wai fa a cewarsu tana kara jefa kanta cikin Matsala ne, domin maganar ma da ta yi a kafar watsa labarai ta BBC HAUSA, Akwai Inda ta jefa kanta.
Ko Shakka babu duk Wanda ya bi wannan balahirar Zai tabbatar da cewa ana ci da gumin Wadannan yaran, musamman Ganin yadda duk wata hira da za ka yi da su marayun za su ce da Kai; " Mu abunda mu Ke Kira a taimake mu a zo a binciki halin da mu Ke ciki, Wallahi muna cikin tashin hankali."
Saura da mi?
Tabbas mu dai mun yi iya na mu yi, kuma ba mu ja baya ba. Sai dai kamar yadda munka fada ne a baya cewa; mun zabi mai Girma Gwamna ne da zummar ya jagorance mu ne zuwa ga turba ta gari, shi kuma ya zakulo wadanda ya ke gani sun cancanta ya ba su wasu mukamai domin su rika masa. Kuma ba wai hakan na nufin duk Wanda gwamnan ya baiwa riko shike nan bai samun nakasu ba, a'a dole wata Rana a samu kasawa ko son rai irin namu na 'yan adama. Wanda in anka kwabe mu sai mu dawo akan dai-dai ko mu saitu akan turba. Amma abunda Ke daurewa duk wani Bazamfare kai, shi ne; Tun Lokacin da anka fara wannan balahirar zuwa yau, ba mu ji wani mataki da ita Gwamnatin mai Girma Gwamna ta dauka da zummar ceto Wadannan bayin Allah da kaddarar Allah ta fado masu, Har sunka zo duniya cikin jarabawar ba tare da sun San uwa, uba ko wani Dan uwa nasu ba. Wanda hakika su Ke matukar bukatar taimako daga duk wani Dan Adam da Allah ya halitta da hankali. Duk cewa duniya kaf! Ta yada Labarin da Wadannan marayun su Ke ciki.
Wanda Saboda samun dama, Har an fara daukar matakin jefa shi Wanda ya fara kwarmato wannan aika-aikar cikin wani hali. Dan haka muna Kira ga Mai Girma Gwamna, da Babbar murya cewa; ya dauki matakin da Zai ceto Wadannan bayin Allah, domin Wallahi sheda na Ke har gaban Allah, bayin Allah din nan suna cikin halin kaka-nika-yi. Wanda muddun ba Kai ka dauki matakin tsamo su ba, to Wallahi za a cigaba da ci-da-guminsu ne, kuma Wallahi Kai Ne sila. Allah Zai tambayeka.
Daga karshe muna Kira kungiyoyin kare hakkin Dan Adam, musamman kungiyoyin kare hakkin Mata da kananan yara na duniya. Da su shigo gidan Marayu na Gusau, domin ceto Wadannan bayin Allah, da Allah ya jarabta da marainantaka.
Da haka, mu Ke rokon Allah ya kawo wa wadannan MARAYU dauki, ya fitar da su daga cikin wannan mummunan halin da su ke ciki, ya maye masu halin da kyakkyawa, ya Allah ka albarkaci rayuwar Wadannan bayi naka, ka yi masu Mafita ta duniya da lahira. Duk Mai kokarin ci-da-guminsu Allah kada ka ba shi abunda ya ke nema duniya da lahira, ya Allah ka hana masa jin dadin kwanciyar kabari, Allahumma amin.
Daga AbdulmaliK Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

