Ganawar Wadda ta samu halartar kusan dukkanin shuwagabannin kungiyar na jahar Zamfara.
A Lokacin da ya ke jawabi, Shugaban kungiyar na Jahar Zamfara Malam, Naziru Buda. Ya yi jawabi kamar haka; "Mai Girma Gwamna kamar yadda ka ke gani, Muna tare da jagororin tafiyar. Na jahar Zamfara kuma wannan tafiya Mun fara ta ne kusan shekara daya, baya. Domin gangamin Neman goyon baya daga gare na ka amince, Dan Allah ka fito. Takarar Gwamna a 2019. Tare da Neman maka goyon Bayan Jama'a daga Al'ummar jahar Zamfara. Wanda mun fara haka ne, Saboda ga Ganin ruhin addini, a dugaduginka.Dan haka muna kyautata zaton a wannan tafiya Akwai alheri.
Saboda wannan muna Neman goyon bayanka da na amincewarka da wannan aikin da munka soma kuma za mu cigaba.
Babban abunda ya kawo mu nan shi Ne ka gana da shuwagabannin wannan kungiyar. Wanda in Allah ya yarda daga assabar din nan za mu fara aikin Neman goyon Bayan mabiya Insha Allahu"
Da anka mai abun magana ga shi maitaimakin Gwamnan
Ya fara mika godiyarsa ga Allah subhanahu wata'allah daga nan ya cigaba da jawabi kamar haka;
"'yan uwa, zan iya cewa nagode. Duk da ban San da wannan tafiya ba, sai dai in gani a online ko Labarin wannan tafiya. A sama-sama ga wasu mutane da abun da kungiyar ta ke kunshe da shi.
"Haka zalika ina godiya da yunkurinku.
Zan so ku san cewa;
"Ban yarda ayi tafiya, ta ni, ba.
Sai dai ayi tafiyarmu. Wanda in Allah ya ba mu nasara a ga cewa an samu nasara mu ne munka samu nasara
Sai dai ayi tafiyarmu. Wanda in Allah ya ba mu nasara a ga cewa an samu nasara mu ne munka samu nasara
"Wallahi maganar mukami Gwamna ko akasinsa, bai wuce zuwa makogarona ba Dan haka ban yarda a lahanda wani ko sanya wani cikin wani hali ba. Dan dai in zama wani ba.
"Tafiya irin wannan duk Wanda ya zo dole a yi hankuri da juna. Domin yanzu anka soma, ku sani wannan tafiya ce, ta akida.
"Allah ya taimaki wannan tafiya, ya ba mu nasara. Ya hada mu a gun soyayyar Allah da Manzonsa."

