Kungiyar Mai suna progressive "Youth Assembly Gusau" ta rubuta wa Kwamishiniyar wannan wasika, ta ofishin kakanin Majalisar dokokin jahar Zamfara. Inda ta yi tur da Allah waddai da Kalaman Kwamishiniyar, tare nuna kalamai ne, masu matukar rashin dadin saurare da ba su cancanci fita daga bakin mace mai kima da ilimi irinta ba.
Kungiyar ta Nemi Kwamishiniyar HAJIYA BALKISU IBRAHIM BUNGUDU ta fito ta Nemi afuwar masarautar Gusau, da dukkanin Al'ummar Gusau. Akan kalamanta na cin mutunci ga Al'ummar Gusau din da ta yi kamar haka;
"'Yan Gusau Shedanu ne"
"Gusau garin 'yan bariki"
"Garin 'yan iska"
Kungiyar ta gindaya wasu hanyoyin da su ke son dole Kwamishiniyar ta bi su domin Neman afuwar. Wadanda sunka hada da shiga gidan rediyon Zamfara da Pride Fm Gusau, ta Nemi afuwa duk Al'ummar Gusau su ji. Haka dole ne ta rubuta cewa haka ba zata sake faruwa a gaba Ba a cewarsu.




