Na tabbatar Duk wani mai imani ya Kalli wannan makarantar sai ya tausayawa Al'ummar da ke Karatu a cikinta.
Baki daya garin Dolen-moriki wannan makarantar kurrum su ke da ita. Ina da yakinin za mu zaci dolen Moriki karamin gari, ne. Sai dai ko daya.
Domin garin ya fi garin Moriki dake da su ke da sarki mai Daraja ta daya. Girma da yawan Jama'a Wanda ke nuna shi kanshi garin zai iya zama karamar hukuma, domin ya wuce matsayin gunduma.
Domin a cikin garin kurrum akwai Rumfar zabe 17.
√ Amma yanzu haka firamarin garin Dolen babu aji daya, da ake Karatu!
√Karkashin innuwar bedi ake karantar da yara!
√ Haka kuma jemagu ne a gurin bedin da ake koyar da yaran!
√ Duka-duka Malamin hudu ne a makarantar Mace 2 namiji 2!
√ Matan dukkansu Hausa su ke karantarwa!
√ Mazan kuma Arabik!
√ Wanda hakan ke nuna matuka bukatar Malamai Musamman masu koyar turanci da lissafi!
Haka zalika kuma akwai matukar hadari a zaman makarantar bigiren da take, yanzu. Domin makarantar na gabda gulbi. Dan haka idan damina tayi babu sauran kwanciyar hankali, ga Malamai da dalibbai uwa uba uwayen yara.
Dan haka muna Kira tun daga Shugaban karamar hukumar Zurmi, Dan Majalissar jaha Mai wakiltarsu da na tarayya. Da ita kanta gwamnatin jahar Zamfara. Da su taimakawa Al'ummar wannan gari. Domin tsamo su, daga wannan mummunan hali da su ke ciki.
Ko ba komi ilimi shi ne gishirin zaman duniya, kuma sai da ilimin ne, mutun kan yi banbancewa tsakanin Fari da baki.
Muna rokon Allah ya sa wannan koke na mu ya kai ga kunnuwan wadanda munka Yi domin su.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta tsakkiya Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496





