Jakadun da Ke marawa, Jakadan jahar Zamfara Comrade NURA ISAH GUSAU baya, sun yi wannan koken ne, domin kara jawo hankalin mai Girma Gwamna da sauran jagororin jahar Zamfara. Dan Ganin cewa Gwamnantin ta marawa, wannan tafiya. la'akkari da yadda tafiyar take kacokan ta jahar Zamfara. Kuma samun nasarar Nura Isah Gusau, ita ce nasarar jahar Zamfara, domin jahar Zamfara ce Ambasada Nura ke wakilta. Kuma abunda Zai samu, matasan jahar Zamfara ne za su amfana da shi.
Dan haka su ke kara mika kokensu ga gwamnatin na Ganin cewa jahar Zamfara ta samu duk wata gudunmawa na Ganin cewa ta yi nasara. Kamar yadda takwarorin jahohinmu Ke marawa wakilansu.





