DAWOWAR SHUGABA MUHAMMADU BUHARI, A NAJERIYA. MU TALAKAWAN KASAR MUNA DA FATA DA YAWA, KANSA.... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 21 August 2017

DAWOWAR SHUGABA MUHAMMADU BUHARI, A NAJERIYA. MU TALAKAWAN KASAR MUNA DA FATA DA YAWA, KANSA....

Bayan dawowar Dattijo sauran mazan Jiya, da a ranar 17 ga watan disamban da ke tafe zai cika shekaru 75, Insha Allahu. ya dawo Najeriya. Bayan shafe kwanaki 103 yana zaman jinya a kasar England.
Da sanyin safiyar ranar da zai sauka 19-8-2017, Mai taimaka masa ta Bangaren watsa Labarai Mr. Femi Adesina, ya Sanar da albishirin dawowar shugaban da Ina ganin yanzu dai ba bu Shugaba mai farin jininsa, a yammacin afrika ko in ce afrika baki daya.
Za mu tabbatar da haka La'akkari da cewa; ni dai a iya tashina ban taba ganin lokacin da Al'umma su ke cikin matsin rayuwa Irin na lokacin mulkinsa na yanzu ba. Amma duk da haka kullum talakawan Najeriya sai kara sonsa su ke yi. Tarbonsa da dunbin talakawa 'yan Najeriya sunka yi a Babban Birnin tarayya a Abuja, sheda ne akan haka.
Kafin dawowar shugaban dai an ta musayar yawo Tsakanin magoya bayansa da akasinsu. Yayinda wasu su ke cewa yana cigaba da murmurewa wasu cewa su ke yi; kwata-kwata shugaban baya cikin hayacinsa, wasu ma sun tabbatar da cewa shugaban ya mutu (a cewarsu) Amma rufa-rufa ce kurrum ake yi....
Daga baya kuma anka shiga takun saka, ta hanyar yin zanga-zangar shugaban sai ya dawo ko kuma ya yi Murabus da wani mawakin kudancin Najeriya da ake yiwa lakani  da "Charlie Boy" ya ta Jagoranta. Duk da magoya bayan shugaban sunyi ta maida martani, ta hanyar shirya zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaban. Baya ga tarin addu'o'in da suke yi masa a lungu da sako na ciki da wajen Najeriya...
Daga karshe dai Allah ya amshi addu'ar mu 'yan Najeriya da sauran wadanda na mara muna baya wajen yi masa addu'o'in samun lafiyar. Saura da mi?
Tabbas mu talakawan Najeriya muna da kwakkwan fata ga SHUGABA MUHAMMADU BUHARI, hakan ma ne, ya sa munka zabe shi ya zamo shugabanmu.
Wanda Alhamdulilahi da hawansa an samu sauki matuka a Bangaren Samar da tsaro, Musamman arewa maso gabas inda rashin tsaron ya fi muni a baya, Alhamdulillahi sai San barka.
Haka zalika Bangaren Samar da saukin rayuwa ga matasa, yana bakin yinsa, shirin NPOWER da anka bullo da shi domin tallafawa matasa zakaran gwajin dafi ne. Sai kuma Bangaren yunkurinsa na karfafawa 'yan Najeriya ta hanyar komawa gona. Wanda Alhamdulilahi duk da gwamnatinsa bata yi wani kwakkwaran tallafi a duk jahohin Najeriya ba.  Bai Hana 'yan Najeriya sunka koma gona ba.
Hakika mu talakawan Najeriya muna da matuka yarda da Aminta tare da shi. Wanda hakan ne, yasa ko da ya kasa mukan yi masa uzuri, domin muna da yakinin ba kansa ya ke yiwa yaki, ba. Dan Haka a kullum mu ke kokari yi masa addu'o'in Allah ya tsare gwamnatinsa, duk wani mai yi mata kutunguila, mu ke rokon Allah ya kawar muna da su.
Kalamai da sunka fito daga bakin shugaban bayan dawowarsa daga jinyar, akan halin da kasarmu take ciki a ranar 21-8-2019, sun nuna cewa; Tabbas shugaban Najeriya ce, a gabansa. Duk da kacokan ya maida hankali ne, ga sha'anin cigaba da zaman Najeriya tsintsiya nadaurinki daya tare da alkawarin Daukar kwakkwaran mataki ga duk wani ko wasu gungun jama'a da ke son kawo rabuwar Kai ko tada zaune tsaye. Wanda hakan kurrum ya tabbatar muna da cewa hankalin shugaban, na kan Najeriyar duk da baya da lafiya a baya. Kuma yana da Gurin cigaban kasar.
Daga karshe muna fatan shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai Kara tsage damtse wajen cigaba da yakar cin hanci da Rashawa, samar wadatacciyar wutar lantarki, bunkasa tattalin arziki, bunkasa Bangaren ilimi, habbaka sha'anin kiyon lafiya, bullowa da wasu hanyoyin da za a taimaki matasa, 'yan kasuwa, mata da matasa ta yadda al'amurran rayuwa za su yi sauki ga talakawan Najeriya.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here