ISLAMIC ONLINE UNIVERSITY DAMAR YIN KARATU KYAUTA GA DALIBBAN JAHOHIN SOKOTO, KEBBI DA KUMA JAHAR ZAMFARA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 23 August 2017

ISLAMIC ONLINE UNIVERSITY DAMAR YIN KARATU KYAUTA GA DALIBBAN JAHOHIN SOKOTO, KEBBI DA KUMA JAHAR ZAMFARA.

ISLAMIC ONLINE UNIVERSITY

DAMAR YIN KARATU KYAUTA GA DALIBBAN JAHOHIN SOKOTO, KEBBI DA KUMA JAHAR ZAMFARA.


Wannan jami'a Mai suna a sama ta bullo da wani muhimmin shiri domin baiwa dalibban jahohin da munka bayyana, damar karatun Diploma, kyauta. Wannan diploma dai ta tsawon shekaru  2 ce tare da yin zangon karatu 4: haka zalika dalibbai za su iya yin karatu a yanar gizo ko akasin haka.  Haka akwai kayan karatu wadatattu da sunka hada littafai da kuma handouts.

Bugu da kari akwai wadatattun malammai da za su iya share ma dalibbai damuwarsu da ma amsa tambayoyin dalibbai ta hanyar wayar salula.

MANUFA
Kashi 60 cikin dari na wadanda za su amfana da wannan damar mata ne anka warewa kason. Kuma Dukkaninsu sai sun kasance mazauna  Sokoto, Kebbi da Zamfara.

TA YA ZAKA IYA ZAMA DALIBI A WANNAN JAMI'A?

Ya kasance dalibi yana fahintar turanci. Haka Dole ne ga dalibi ya kasance yana da kyakkyawan Sakamakon Jarabawar  Kare babbar Makarantar Sikandire, akalla ya kasance yana da credits uku hadi da Mathematics da kuma English.

MU KULA; Dole ne dalibi ya cike form na yana neman damar karatu a wannan jami'a tare bayarwa ga Wakilanmu da ke jahohin; Sokoto, Kebbi da Zamfara.

ZA A SAMU FORM DIN SHIGA MAKARANTAR, TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA;

Sokoto; A IOU Coordination Center No. 1 Katsina Road, Off Emir Yahaya Road, Sokoto 08063233285, 07062564866

Kebbi; A Bafakke Int’l Ventures, Milton Plaza, Opp. School of Nursing, Birnin Kebbi 08131328000

Zamfara; A No. 38 Sadiqu Sadiq Road, Opp. State Pension Board, Gusau 07037890013

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here