Dari bisa dari na ke son Jahar Zamfara, babu garwaye.
Dan haka Dan/'Yar uwa kada ma ku fassara ni a hagunce. Sai dai in ce ku bi rubutuna da kyau.
A wannan karnin irin yadda gwamnatin Jahar Zamfara ke yiwa harkar ilimi RIKON SAKAINAR KASHI. Ko a tarihin kasar nan ban taba jin wata Jahar da ta yi ko rabinsa ba. Ina da yakinin wannan tabbataccen sanannen abu ne, ga kusan dukkanin Zamfarawa. Dan haka ba bukatar Karin haske....
Sai dai zan dan bada misalai akan wasu taimakon da irin wadannan kungiyoyin sunka yi a jahar Zamfara, amma kiri-kira gwamnan jahar Zamfara ba ya nuna goyon bayansa ga wadannan shiraruwa.
Farawa da yunkurin, hukumar UNICEF, na tallafawa mata su zurfafa karatunsu. Wanda wannan yunkuri ne, Mai kyau. Dan ganin muhimmancin ilimin 'ya mace. Amma kiri-kira tun da anka Fara wannan shiri a shekara ta 2013, ya ke fuskantar matsaloli Wanda har hakan ya fara barazana ga karatun su dalibban da anka dauka. Kuma hakan ne ma muke tunanen sanadiyar da ya sa tun daga dalibban farko na wannan shirin ba a kara daukar wasu ba....
Haka a shekarar da ta shude hukumar TDP (teachers development program) ta zabi jahohi uku a arewacin Najeriya http://www.tdpnigeria.org/ jigawa . Domin fara jaraba wani tsarin koyarwa na musamman ga Malamai da dalibban NCE masu koyon sanin makamar koyarwa, Wanda a lokacin Kungiyar ta zabo dalibbai masu hazaka daga bangarori daban-daban. Tare da ba su horo na musamman akan Sabon tsarin.
Tare da tura su a makarantanni domin Gwaji! Wanda Alhamdulillahi ina cikin wadannan dalibbai kuma Alhamdulillahi, mun samu nasara Kwarai da gaske a lokacin. Wanda ina da yakinin da gwamnatin Jahar Zamfara za ta maida hankali ga wannan tsarin to wallahi da gibin da anka yi muna, tuni za mu cike shi. Amma ina. Har yanzu gwamnatin jaha zamfara ba ta sanya hannu a wannan shirin ba, wanda yanzu haka da dama daga cikin dalibban da anka zabo Domin wannan shirin da wahalar gaske su shiga cikin shirin. Wanda wannan ke nuna sai dai hukumar ta yi barnar kudinta, ga banza kenan. Tunda sun koyar da mu, amma haka abunda sunka koyar da mu zai tafi a banza....
Haka a cikin wannan watan Na shekarar da ta shude 2016 ne anka ruwaito,
Gomnan jihar Zamfara Alh. Abdulazeez Yari Abubakar inda yake koyawa Yara karatu a wata firamare da ke Maru (Banaga Model Primary school) bayan ya koya ma wasu a Abubakar Tunau Primary school Talatar Mafara.
Gomnan jihar Zamfara Alh. Abdulazeez Yari Abubakar inda yake koyawa Yara karatu a wata firamare da ke Maru (Banaga Model Primary school) bayan ya koya ma wasu a Abubakar Tunau Primary school Talatar Mafara.
Shehi ya koya masu karatun ne a lokacin Kaddamar da wani dakin karatu Na zamani wato e-library da wata kungiya mai zaman kanta ta samar a Makarantun biyu. Wannan Abu ne mai matukar muhimmanci, amma matsalar a nan ita ce, shin Malam makarantannin ma an samar masu da kwamfutar!?
Shin Malam sunma iya kwamfutar?
Shin Akwai kayan aikin da za a cigaba da kula da kwamfutocin?
Wane kokari gwamnatin ta yi na samar da injimomin samar da wutar lantarki a wannan makarantanni, Musanman na Maru??
Shin daga Shekarar da ta shude zuwa yanzu wane cigaba ne anka samu a wadannan makarantannin?
Anya kayan aikin ma suna nan Kuwa?
Wanda ina da yakinin wadannan shiraruwa da a wasu jahohin ne, da gwamnonin jahohin za su rungume su hannu biyu-biyu. Dan bunkasa harkar ilimi a jahohin. Amma mu a jahar Zamfara, ba wani takamammen yunkuri da gwamnatin ke yi na kawowa Jahar cigaba ta Bangaren ilimi, in har sun zo sai dai su yi kidinsu su yi rawarsu, hade da kururuwar neman Wanda zai zo kallonsu. Wannan kenan!
Wallahi dole mu fito mu fadi wa gwamnatin Jahar Zamfara gaskiya, shi zai sai ta gyara kura-kurrai da take tabkawa. Amma zura ido shi zai sa su cigaba da yi muna kisan mummuke.
Allah ya kyauta, ya Allah muna rokonka da ka daukaki Jahar Zamfara tare da al'ummarta, a duk inda su ke.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

