SHEKARU 3 DA KARBEWA TALAKAWAN JANGEBE GIDAJE DA FILAYE, ANKA YI MAKARANTAR 'YAN MATA. AMMA HAR YANZU BA A BIYA SU, HAKKOKINSU BA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 10 August 2017

SHEKARU 3 DA KARBEWA TALAKAWAN JANGEBE GIDAJE DA FILAYE, ANKA YI MAKARANTAR 'YAN MATA. AMMA HAR YANZU BA A BIYA SU, HAKKOKINSU BA!



Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

Tun a 2014 ne Gwamnati ta Auna, filaye 226 da Gidajen Al'umma 4 a Karamar hukumar Talatar Mafara a Gundumar Jangebe. Domin yin Karamar Makarantar Gwamnatin tarayya ta 'Yan Mata da ke Jangebe.

Wanda tuni an gine filayen har Makarantar ta Fara aiki. Amma sai dai kash! Har yanzu ba a biya su mamallaka wadannan filayen da gidajen kudinsu na diya ba .

Kullum  ma'aikatar filaye da safiyo ta Jahar Zamfara gobe-gobe take yiwa wadannan mutane. Duk da cewa,  mutanen na tsammanin tuni an biya su kudadensu. Amma har yanzu  naira bata zo gun mamallaka wadannan hakkokin ba.



Dan Haka muna Kira ga Gwamnatin Jahar Zamfara karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI MAFARA da kwamishinan filaye da safiyo.

Da su ne kacokan nauyin biyan wadannan mutanen ya rataya a wuyansu, da su dibi girman Allah. Su biyawa wadannan bayin Allah hakkokinsu. Musamman Ganin cewa akwai wadanda suna cikin gidajensu anka tayar da su. Wanda yanzu suna cikin tashin hankalin rashin gidajensu.


Daga karshe, muna Rokon Allah ya sa wannan koke na mu ya Kai ga kunnuwan da munka yi domin su. Su kuma Allah ya ba su ikon share muna hawayenmu. Allahumma amin.



Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here