HANNUNKA MAI SANDA.... BAYAN RUWANDORUWA YA KASA, WAYE YA KAMATA MU ZABA, YA MAYE GURBIN.... A 2019? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 10 August 2017

HANNUNKA MAI SANDA.... BAYAN RUWANDORUWA YA KASA, WAYE YA KAMATA MU ZABA, YA MAYE GURBIN.... A 2019?

Daga; Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

Tun bayan da munka fito kwanmu da kwarkwatarmu, munka zabi 'Da ga Babban Attajirin nan na Jahar Zamfara, Wato Alh. Ibrahim Ruwandoruwa.

Wanda sunka fafata da takwaransa, Mahadi Ali Gusau Na jam'iyar PDP Wanda wasu ke Ganin Isah Ibrahim Ruwandoruwa Doruwa ya samu Galaba ne, saboda abu uku na farko dai mahaifin Isan ya kasance daya daga cikin attajiran da talakawa Ke amfana da Dukiyarsa. Wanda saboda Haka ne, Al'umma Na zabe dansa...

Na biyu, kwata-kwata Mahadi bai da wata kwakkwarar sani akan Al'ummar da zai wakilta. Uwa-uba matsalolin Al'ummar Gusau da Tsafe. Wanda wasu na Ganin shi ne silar da ya sa Al'ummar Gusau da Tsafe sunka ki zaben 'Da ga Janaral Aliyu Muhammadu Gusau (Mai Murabus)

Sai dai wasu na Ganin cewa guguwar Shugaba Buhari ce ta sanya Isah Ibrahim Ruwandoruwa, ya yi Nasara kamar yadda Takwarorinsa na jam'iyar APC sunka yi a 2015....

Ko dai mene ne, a wannan iskar Mai kadawa Isah Ibrahim Ruwandoruwa ne, ke wakiltar kananan hukumomin Gusau da Tsafe a Majalisar Wakilai ta tarayya.

Sai dai wasu na Ganin cewa wakilin ya kasa, Tun daga Bangaren rashin isar da koken Al'ummar da sunka zabe shi, a Majalisar. Da kuma rashin kyakkyawan wakilci Wanda ake zargin Isah Ibrahim Ruwandoruwa da yi.

Wanda hakan ne, ya sa Al'ummar Gusau da Tsafe, munka yo caaaa! Ido rufe, Da zummar zakulo Wanda Zai iya a 2019 in Mai ni da ku ya so....


Sai dai wani hanzari ba gudu ba.

Wane kalar Dan siyasa ne, mu ke so a 2019?


Cancanta za mu bi, kudi, ko gata?

Matashi mu ke so ko Tsohon kwano?


Shakka babu dole mu yi karatun ta natsu, Dan kadda mu yi kitso da kwarkwata. Kadda mu yarda a YI muna sakkiyar da ba ruwa a 2019, kadda mu yarda da masu dadin baki da sunan yaudararmu....


Tabbas muna bukatar matashin Mai ilimi wayayye da zai iya Kai kokenmu, Amma fa Wallahi jajirtacce, Tabbas muna bukatar matashi Amma fa amintacce, nagartacce Wanda duniya ta sheda da adalci da kokarin kwatantata Gaskiya.

Ba Matashin da za mu zaba ya kara samun damar yaudararmu ba.


SHAWARA ZUWA GAREKA DAN TAKARARMU....


A yanzu akwai yan takara wadanda lissafi na bai san iyakarsu ba. Da ke rigoguwar wannan kujerar ta Gusau da Tsafe. Sai dai cikinsu Wallahi akwai wadanda ko in ce gwamma Isah da shi.

To Ina Ba ku ko Kai SHAWARA DA Dan Allah ka yiwa kanka kiyamullaili ka koma gefe. Domin Wallahi in dai muna raye ba za ka yaudari Al'ummar Gusau da Tsafe muna gani ba.

In kuma ka ki ji to za mu so ka CIGABA.  da nuna maitarka a fili.... Mu kuma za mu bayyanawa duniya ko Kai WAYE....

Kukan kurciya ne, na ke yi. Mai hankalin ne ZAI fahinci abunda na KE YI.

Saura da mi in kunne ya ji zan iya cewa gangar jiki ta tsira....


Post Bottom Ad

Responsive Ads Here