KUNGIYAR MATASAN ZAMFARA TA TSAKKIYA TA YI KIRA GA SHUWAGABANNI DA 'YAN SIYASA SU TAIMAKI MATASA MASU SON KOMAWA MAKARANTA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 26 October 2017

KUNGIYAR MATASAN ZAMFARA TA TSAKKIYA TA YI KIRA GA SHUWAGABANNI DA 'YAN SIYASA SU TAIMAKI MATASA MASU SON KOMAWA MAKARANTA!

Shugaban kungiyar ne na Jahar Zamfara Rufai UB Gusau(Shattiman magazu), ne ya bayyana haka, inda ya kira ga shugabanni da 'yan siyasa dama masu hannu da shuninmu da su dauki dabi'ar tallafawa matasa . Musamman a Bangarorin neman ilimi Samar da ayukkan yi da kuma wayarwa matasa kai akan biyar tafarki nagari.


Shattiman na magazu ya yi wannan kiran ne, a lokacin da ake tattaunawa kai tsaye da shi akan manufar kungiyar matasan zamfara ta Tsakkiya, tare da amsa wasu daga cikin tambayin  da sunka shafi kungiyar.

A cewarsa "Kungiyar matasan zamfara ta Tsakkiya zata yi bakin kokarinta wajen biya matasa kudaden Makaranta tare da ba su scholarship. Haka zalika za ta bullo da shiraruwa da za su taimaki rayuwar matasan.

"Daga nan ya yi kira ga shugabanni, 'yan siyasa da kuma masu hannu da shuninmu da su dauki dabi'ar tallafawa matasa su yi karatu. Musamman Ganin cewa akwai matasa da dama da ke son yin karatu, amma Dan abunda bai taka kara ya karya ba ya hanasu yinsa" a cewarsa.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here