WASU DAGA CIKIN YAƘOƘAN DA KAFURAI SUKA SHIRYA
Daga cikin fitattun yakokan da kafurai suka shirya akwai
1- Yakin Duniya na daya wanda aka fara daga 1914 zuwa 1918 wanda wannan yakin yayi sanadiyar zubarda jinin mutun 17,000000 hadi da jikkata mutun 10,000000. inda wasu daga cikin mutanen sun nakkasa sunzama musakai, sunrasa gidajensu, Wanda wannan yakin bawai musulmai ne suka fafataba a a kasashen turawa sukayi wannan fadan kuma duniya tasan dashi amma an manta da wannan taaddanci da suka tafka Kuma baa alakanta addinin wadanda sukayi wannan yakin da taaddanci.
2-Yakin Basasar kasar rasha (Russian Civil War) wanda akayi daga shekarar 1917 zuwa 1922 tsakanin yan gurguzu da sojojin dake biyayya ga sarkin gargajiyar rasha na wancan lokacin wanda wannan yakin yayi sanadiyar zubarda jini tare da halakarda a kalla mutun 5,000000, shima wannan duk ba taaddanci bane kuma duniya bazata tunashi ba, tare da bayyana yan gurguzu a matsayin yan taaddaba ba.
3- Yakin duniya na biyu wanda akayi daga shekarar 1939 zuwa 1945 inda aka gwabza tsakanin su hitler yan gurguzu, dakuma yan jari hujja wato su wintson Churchill dakuma Franklin roosevelt, inda mutun million 36 zuwa million 40 suka mutu amma duniya ta mance da taaddancin da wadannan mutanen sukayi.
Kuma bazaa kira addininsu malaman da suka cusawa wadannan mutanen wadannan akidun ba. irinsu Karl Marx da da irinsu George Washington, Benjamin Franklin hadi da jami'o'in da sukayi karatu a matsayin yan taaddaba ba sai musulmai.
kuma bazaa kira gyara manhaji dakuma manjahar karatun da sukayi a matsayin mai cusawa mutane taaddanci ba.
4-Yakin Sino-Japanese II wanda akayi tsakanin China da Japan daga 1937 zuwa 1945. Inda yakin ya lakumi rayukan mutane har 20,000000 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu hadi da jikkata su shima wannan duk ba taaddanci bane.
5- Yakin basasa na kasar China wato (Chinese civil war) wanda aka fara daga 1947 zuwa 1949 wanda akayi tsakanin shuwagabannin China na wancan lokacin dakuma hadakar yan gurguzu wanda aka kashe mutane 6,000000 inda daga karshe yan gurguzu suka samu nasarar data basu damar kafa gwamnati a China har zuwa yau, amma su bazaa kirasu yan taaddaba ba.
6- Harin Hiroshima da Nagasaki wanda america ta jefa (atomic bomb) a wadannan yankunan na kasar Japan a cikin watan augustan shekara ta 1945.
Jim kadan bayan kammala yakin duniya na biyu, wanda wannan bomb din anjefashi ne tare da sa hannun shugaban kasar america na wancan lokacin wanda ake kira Franklin roosevelt. Inda bomb din yayi sanadiyar kashe Akalla 129,000 tare da jikkata dubun dubatar mutane, hadi da yada cututtuka na tsatso sakamakon gurbacewar muhalli, amma duniya bazata rika tunawa da shugaban amurka na wannan lokacin ba a matsayin dan taaddaba sai musulmai.
7- Akwai yakin daya afku daga shekarar 1955 zuwa 1975 tsakanin yankokan kasar Vietnam biyu. Wato arewacin Vietnam (north Vietnam) dakuma kudancin Vietnam (south Vietnam), wanda a wannan yakin kasashen irinsu china, rasha da sauran kasashe masu bin tsarin gurguzu suna goyon bayan arewacin kasar Vietnam ne, Inda sukuma kasashen dake bin raayin jari hujjanci dakuma demokradiyya irinsu amurka, koriya ta kudu da sauransu suka goyi bayan yankin kuduncin kasar Vietnam inda aka gwabza yakin da yayi sanadiyar mutuwar mutane daga 1,000000 zuwa 2,000000 wadanda suka yi tarayya a wannan yakin suma ba yan taadda bane ko sai musulmai.
8- A shekarar 1975 tsohuwar tarayyar Soviet tayi yunkurin fadada mulkin gurguzu (communism) zuwa kasar Afghanistan inda kasar america da kawayenta suka zama munafukai sai suka tsaya tsakiya inda suka tallafawa gwamnatin mujahidun ta kasar Afghanistan a wancan lokacin.
Inda cikin Allah mujahidun suka yi nasara ga tarayyar soviet ta wancan lokacin (Russia). Wanda a wancan lokacin ana kiran mujahidun din Afghanistan da sunan mayakan yanci (freedom fighters), wanda daga karshe da tarayyar soviet taga ba sarki sai Allah sai ta kwashe kayayyakin yakinta ta fita kasar.
Bayan fitarta sai amurka da kawayenta suka kulla yaki da Gwamnatin da take bin shariar musulunci ta mujahidun karkashin jagorancin Moula Umar da zimmar ganin bayansu dakuma kafa demokradiyya a kasar.
Daganan kuma sai Amurka ta ayyana gwamnatin (Taliban) a matsayin gwamnatin yan taadda sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a tagwayen gineginen cibiyar kasuwancin duniya dake birnin New York dake amurka, inda aka alakanta wannan harin ga mujahidun din Afghanistan.
Bayan kuma sun ayyana cewa basu suka kai wadannan hare haren ba dayayi sanadiyar kashe mutane a kalla 2,996 inda mutane 6,000 suka jikkata.
kawai dai anshafa masu kashin kajine, daga nan sai gwamnatin amurka karkashin jagorancin (George W Bush) ta wancan lokacin ta kaddamar da wani shiri da ake kira (war against terrorism) wato yaki da taaddanci a shekarar 2001.
Inda tayi amfani da wannan damar ta harin September 11 a matsayin hujjar yakar mujahidun din Afghanistan.
Dakuma ganin cewa an mika masu Osama Bin Laden wanda sukace shine ya kitsa harin taaddancin "September 11". Wanda haryau wannan yakin ne aketayi da sauran burbushin mujahidun dinda suka rage a kasarta Afghanistan.
Duk da cewa amurka tasamu nasarar kafa demokradiyya a sassan kasar, inda take da kudurin jaye sojojin kasarta daga Afghanistan din idan taga ta iyarda karya lagon wadannan mujahidun din kwata-kwata.
Wanda wannan yakin yayi sanadiyar kashe a kalla mutane yan Afghanistan 36,000 zuwa 50,000 tare da jikkata kusan mutane 1,000000. Amma bamuji ana alakanta taaddanci ga kasashen gurguzu da yan jari hujja ba wadanda sune silar fadawar wannan kasar yakin da take ciki haryau.
YAKE YAKEN DA WASU AL AMURRA DA SUKA BIYU BAYAN (War Against Terrorism)
1- Yakin (Gulf War) wanda yakawo karshen mulkin gurguzu a kasar Iraq dakuma mika mulki ga yan shia a bisa tsarin demokradiyya.
2- Juyin Juya Tunisia
3- Juyin juya halin Masar Wanda yabawa sojoji damar karbe mulki, inda (Alfata al sisa) yazama shugaban kasa ta hanyar juyin mulki daga bisani Kuma ya rikide yazama dan demokradiyya (farar hula).
5- Wanke kwakwalen wasu daga cikin yan kasar libya tare da basu makamai inda har suka kai ga yakar gwamnatin Gaddafi, wanda kowa yasani dasa hannun kasashen turawa gurin samarda rashin daidaituwar al amurran siyasa a kasar ta Libya har zuwa yau.
6- Rikicin Syria Wanda shima rashin kawo karshen shi har zuwa yau. Yanada alaka da tasirin kasashen turawa masu bin tsarin demokradiyya da gurguzu sukayi. Wanda mafi akasarin wadannan yakokan anayinsu don kawai aga bayan musulunci da musulmai.
Sannan duk masu kurarin cewa wai musulmai sune yan taadda, shin waina makaman da ake aiki dasu gurin taaddanci waye ya kirkiresu?
Musulmai ko kafurai?
Sannna kasashe masu makamin nuclear hadi da karfin soji guda nawane a cikin kasashen musulmai?
Sannan tayaya musulmai suka zama yan taadda bayan a cikin tarihin musulunci tundaga zamanin Annabi Muhammad (saw) har zuwa babu musulmin dayayi yakin da yakashe mutane koda 500,000 idan kuma akwai shi a fada manashi.
Donhaka yakamata yan uwana musulmai musani jefa kalmar taaddanci ga musulunci kasani rashin adalci ne dakuma shafawa musulunci kashin kaji da turawa keyi donhaka kadena rakiyar su.
Wanda idan mutun ya karanta wannan dan ƙaramin rubutun zai tabbatar da cewa lallai wannan kalmar da ake jinginawa ga musulmai zalunci ne dakuma yakarsu da akeso ayi gadan gadan. Wanda idan muka lura duniya ta hadewa musulmai kai a wannan lokacin.
Sannan a kullum abunda yake kara tabbata a zuciyata shine da ace addinin musulunci ba gaskia bane, kuma da Allah baiyi alkawalin cika hasken sa a doron kasa ba, wallahi ina mai yarda cewa da tuni Addinin nan yazama tarihi.
25/10/2017
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Tuesday, 24 October 2017
Home
Unlabelled
TSAKANIN MUSULMAI DA MASU RAAYIN GURGUZU DA JARI HUJJANCI SUWAYE SUKAFI ZAMA BARAZANA GA ZAMAN LAFIYAR DUNIYA A WANNAN ƘARNIN.
TSAKANIN MUSULMAI DA MASU RAAYIN GURGUZU DA JARI HUJJANCI SUWAYE SUKAFI ZAMA BARAZANA GA ZAMAN LAFIYAR DUNIYA A WANNAN ƘARNIN.
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

