A fahinta ta adawa na nufin tsayuwa akan tafarki na Gwaggwarmayar tsamo Al'umma akan tafiyar da mulki. Wanda da farko za ka nemi mulkin da zummar Jagoranci nagari, in ka fadi zabe sai ka koma gefe kana sanya Ido duk lokacin da gwamnatin ta dauki wani shiri da ke da Illa ga al'umma ko ta yi yunkurin tauye wani haki Na Al'ummar. Sai ka fito ka soki lamirinta tare nuna illar hakan, Wanda hakan zai sa ta yi takatsantsan wajen tafiyar da mulki. Wanda har wasu kena ganin 'yan adawa su ne adon mulkin dimokadiyar. Domin idan babu 'yan adawa a mulkin dimokadiyar zai kasance kamar mulkin Soji ko na Kama karya!
Amma dai dai Kash! A Jahar zamfara muna da wasu rubabbun mutane da ke kiran kansu 'ya adawa a jam'iyunmu daban, Amma Idan ka debe Tsohon Sanata wanda ya wakilci Zamfara ta Tsakkiya. Ba wani dan siyasa da ke fitowa ya fadi, Illa ta Gwamnatin Jahar ZAMFARA Mai ci a yanzu ko sukar gwamnati akan wani abu da ta yi da bai dace ba.
Wanda ko shi ba zan iya bugun gaba in ce, dari-bisa-dari ya yi abunda ya dace ba. Ganin cewa Matsalar rashin tsaro dai ce a lokacin ya maida hankali kanta, ba tare da ya yi Magana akan abunda ke kawo Matsalar ba. Sai dai dole mu yaba masa, domin ba mu taba samun irinsa ba. Wannan kenan!
Sai dai TAMBAYOYIN mu ga wadanda ke kiran kansu 'yan adawa a Jahar Zamfara su ne;
Shin kun gamsu da kamun luddayin Gwamna ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI MAFARA?
In kun gamsu, sai mu ce manufarku daya da shi Kenan, inda kaddarar Allah ta sa kun kai ga madafon ikon da haka kuma za ku YI muna kenan ko?
Za ku kyale 'ya'yan talakawan Jahar a yashe ba madogara ko?
Za ku ki biyan WAEC DA NECO ko?
Za ku ki taimakawa matasa su nemi ilimi ko?
Za ku azabtar da ma'aikata ko?
Za ku yi muna mulki a hangunce kamar yadda ya Ke yi YANZU ko?
In ba ku yarda da kamun luddayin ba!
Me ku ke nufi da mu?
Shin sai an buga gangar siyasar 2019 ku fito kuna cewa ya kasa, ku za ku iya?
A kullum Ina da yarda da yakinin cewa mafiya yawansu ba danmu su ke neman mulki ba, haka adawar ma ba Dan mu su ke yi ba.
A kullum sai ka ji ana fadin akwai Manya-manyan 'yan adawa a jam'iyar PDP, APGA da sauran kananan jam'iyu. A kullum za ka ji suna bugun gaba wai su 'yan adawa ne.
Sai dai baka taba ganin suna nuna adawarsu, sai lokacin da yakin neman zabe ya tusgo...
Wanda a zahirance a hankalce lokacin da ake gudanar da mulki ne, a take da amfani. Domin a lokacin da gwamnati ta yi abunda bai dace ba, sai 'yan adawa su fito su yi adawa da abun Dan cilastawa gwamnati ta dauki matakin dawo kan turba.
Amma kiri-kiri Dan 'yan adawar jahar Zamfara sun mayar da mu talakawan Jahar zamfara jahillai, sai ka tarar kwata-kwata 'yan adawar jahar sukan bar jahar da sun fadi zabe. Ba ka koma jinsu sai kuma lokacin zaben ya dawo. Inda za ka ji sun fito, suna cacar baki wai gwamnati ta kasa waje kaza ta yi maku kaza! Wanda kwata-kwata hakan na nuna cewa ba wai mu ne gabansu ba. Wanda kamar yadda na fada da mu ne a gabansu da ba za su bar jahar ba, za su tsaya ne, cikin Al'ummarsu su cigaba da adawa dan tsamo Al'ummar Jahar tare da dora Jahar akan turba ta gari.
Dan Haka muna Kira ga 'yan adawar jahar zamfara da su sani cewa ba, kan mage ya waye. In dai Dan mu ku ke yi to YANZU za ku yi wa mu talakawan aiki. Ba lokacin zabe ba.
Allah ka taimaki Al'ummar Jahar ZAMFARA, ka iyawa talakawan Jahar, ka kawar muna da duk makiyanmu. Duk Wanda ke da gurin cutar da mu duk jam'iyar da ya ke, Allah ka yi muna maganinsa. Allahumma amin.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
23-10-2017
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Monday, 23 October 2017
Home
Unlabelled
MAFIYA YAWAN 'YAN ADAWAR JAHAR ZAMFARA, BA JAHAR CE GABANSU BA! ILLA 'YA'YANSU DA KAWUNANSU.
MAFIYA YAWAN 'YAN ADAWAR JAHAR ZAMFARA, BA JAHAR CE GABANSU BA! ILLA 'YA'YANSU DA KAWUNANSU.
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

