GAMAYYAR KUNGIYOYIN AREWA (CNG) TAYI KIRA A HANA SAYAR DA MAGANIN MURA BA BISA ’KA’IDA BA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 17 October 2017

GAMAYYAR KUNGIYOYIN AREWA (CNG) TAYI KIRA A HANA SAYAR DA MAGANIN MURA BA BISA ’KA’IDA BA!

Coalition of Northern Groups, Wato (CNG) tayi kira ga Gwamnonin Arewa 19, da cewa akwai bukatar kulle Kasuwannin Masu Sayar da Kwaya Barkatai a Arewacin Najeriya, wannan kiran ya biyo bayan bayanin da Sanatan Najeria yayi na nuna damuwa saboda ana samun fiye da Kwalabe MILIYAN UKU Na #Codeine duk rana a jahar Kano kawai.

Kungiyar CNG Tace ya kamata ace Gwamnonin Arewa masu nuna damuwa ga mutanensu, su kulle wadannan kasuwannin sayar da kwaya barkatai , ba bisa ka’ida ba kuma su gaggauta aiwatar da dokar National Drug Distribution Guidelines (NDDG) wadda Minista mai kula da Sha’anin Lafiya ta kasa basu samar da wannan tsare na sayar da Kwaya barkatarba, kuma dokar kasarnan bata karfafi wannan sana’a ba.

Mai magana da yawun Gamayyar Kungiyoyin Arewa, Abdul-azeez Suleiman ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a Kaduna ranar Jumu’a cewa; " Muna tsammanin dukkanin Jahohin Arewacin Najeriya za su Samar da doka mai karfin gaske dangane da wannan Matsalar ta sayar da Miyagun Kwayoyi barkatai kuma ba kan ka’ida ba," Malam Abdul-azeez ya ce "Dokar ta kunshi hana sayar da jabun  Magunguna da  gurbataccin Sarrafaffen Aminci, kuma a hukunta duk wanda ya saba wannan dokar"


"Sannan a matakin kananan hukumomi, Jaha da Kasa, shirin  (health insurance scheme - wato Shirin Inshorar Lafiya) su samar da Isassun Magani a dukkanin Asibitoci da dakunan Shan Magani domin tabbatar da Mutan Arewa suna samun Ingatattun magunguna"
"CNG ta damu matuka, ganin cewa bayan an gabatar da Jawaban Kaduna (Kaduna Declaration) watannnin da suka wuce, Kasuwannin Jabun Magunguna, Gurbatattun Magunguna da Miyagun Kwayoyi sai kara habaka takeyi a Arewa, daga wasu batagari kuma miyagun ’yan kasuwan"

Bayanin yayi tsokaci cewa CNG ta lura da budaddiyar kasuwar Magunguna misali a Kasuwar Sabon Gari, dake Kano, ya haifar da Shan miyagun Kwayu, Saye da Sayarwar Magungunan Sata, da kuma Kasuwancin magungunan da kasashen ketare suka bayar kyauta (misali Waqee’ar AZITHROMYCIN na kasar Nijar).
Gamayyar Kungiyoyin tace, "Mun damu da Sayar Jabun Magani, Shaye-Shaye da kuma abubuwan da Shaye-Shayen suke haifarwa ga Lafiya, a Syasance, Ga Tattalin Arzikinmu, kai har da ma haifar da Rashin.Tsaro a wannan yankin na Arewa".

"Matsalar Tsaron: rashin kula da masu sufari, sayarwa da tu’ammuli da miyagun kwayoyi, muna ganin ya faru ne domin masu sayar da miyagun kwayoyin su harfar da juyewar kwakwalwar mutanenmu don su fada cikin miyagun halaye da ta’addanci"

"Zamantakewa: Kawo.wannan kasuwar kwaya a Arewa nada manufar bata kyakkyawar alaka da zaman lafiya da lumana da akasan mutan Arewa dashi"

"A Siyasance:Shaye-Shaye da kawo irin wadannan maganin a Arewa anyi ne da gangan domin durkusar da Arewa, Ganin cewa mukeda basirar gudanarwa/Aiwatar da mulki, idan akayi la’akari da bayanai da binciken  WHO suka bayar cewa KANO itace Jahar da akafi sayarda Jabun Maganin Ciyon Zazzabin Cizon Sauro a Africa, kai harma duniya baki daya"
"Tattalin Arziki: Kasancewar Arewa a matsayin yankin da yafi kowane sayen wadannan kayan, Tattalin arzikin Arewa nayin kasa sosai sanadiyar wannan kakagida da ’yan wasu yankin sukayi ga wannan sana’a tareda gurbata sana’ar"

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here