Kamar yadda munka sani cewa yanzu muna rayuwa ne a karkashin wata bahaguwar gwamnati da kwata-kwata ba mu ne gabanta ba. To ya zama dole gare mu yi karatun ta natsu.
Na farko dai dole mu jajirce, domin inganta rayuwarmu. KAMAR ya kenan?
1- ILIMI;
Ilimi shi ne gishirin zaman duniya, to ya zama dole gare, mu tashi mu nemi ilimi na addini da kuma na zamani, na addini zai taimaka muna wajen bautar mahaliccinmu, na zamanin kuma zai taimaka muna wajen huldodinmu na neman abinci, in mun kyautata, Zai taimake mu har a gobe kiyama.
Kamar yadda kunka sani akwai wahala matuka, Tun daga neman karatun har zuwa kashe-kashen kudin a Yayin yinsa. To 'yan uwa kada mu ja baya.
Kadda mu Kalli wasu jahohin Najeriya cewa gwamnatocinsu na taimaka masu, gun neman ilimin. Mu ce dole in ba a yi muna ba sai dai mu ki karatun. A,a mu dauka cewa wannan wata jarabawa ce, Allah ya yi muna, kuma da ikonsa za mu ci.
Dan haka mu sanyawa rayuwarmu cewa za mu yi domin arziki na gunsa zai arzutamu da abunda za mu dauki lalurar kanmu. Wanda watan wata rana za a wayi Gari, abun ya zama labari, har mu ci gajiyarsa!
Amma muddun munka ce ba mu iyawa, to Tabbas abun Nema ya samu gunsu, domin dama gurinsu shi ne; su bautar da mu haka 'ya'yansu su bautar da mu. Domin in ba mu da ilimin ba mu ma sanin su waye mu, balantana hakkokinmu da ke kan jagororinmu Uwa-uba jagorancin ya zo hannunmu.
2- AIKIN YI.
Mun shedi cewa Gwamnatin Jahar ZAMFARA ba ta da wani gurin Samarwa matasan Jahar aikin yi. Domin ta kashe hanyoyin koyawa matasa ayukkan hannu Mallakar Jahar baki daya, haka zalika tunda ta hau mulki bata dauki daya aiki ko ta Samarwa matashi daya hanyar da zai dogara da kansa ba.
Alhamdulillahi bayan wuya sai dadi haka wuya bata kisa. Kada mu dogara sai ta ba mu aikin yi ko hanyar samunsa. Waya Allah mun tafi Makarantar ne, ko kuma Allah bai nufi mun leka ba.
Mu tabbatar da cewa 'yan kananan ayukkan hannu mun rike su, haka sana'o'inmu da ba mu bukatar baban jari ne ko babu jarin ne, kada mu Rena su. Mu rungume su hannu biyu-biyu su ne kimar mu wata ranar za mu zama manyan masu kudi sanadiyarsu, ko ba komi Hausawa sun ce mai karami wata ranar shi ne da babba.
3- TARBIYA;
Duk Wanda ya kalli take-taken Gwamnatin Jahar ZAMFARA na yanzu zai tabbatar da cewa, ba tarbiyar matasa ce ta sanya a gaba ba, duk da cewa dai Tarbiya ita ce ginshiki na zama lafiya. Domin duk matashin da ya rasa Tarbiya ko mai bashi ita, to fa ya shiga uku. Domin in dai ba wani nufi na Allah ba, da wahala ya mori rayuwarsa. Haka zalika zai zama koma baya a dukkanin al'amurransa.
Dan Haka dan uwa matashi, ka sanya dogon tunane tare da hango gaba.
Anya ka taba ganin masu shaye-shaye, 'yan caca, Barayi, wadanda ba su biyayya ga iyaye da na gaba da su da sauran ayukkan assha!, sun zama wasu a rayuwa?
Na san za ce a,a.
Dan Haka dan uwa matashi yi kokarin tashi ka taimaki kanka Dan nemawa rayuwarka ta duniya da lahira makoma.
Allah ka taimaki matashin Jahar Zamfara ka yi mashi Mafita, ka zaba mashi shuwagabanni adillai da za su dora shi kan turba mai dorewa.
Dan uwanka a kullum; Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08

