Mukaddashin darakkatan hulda da jama'a na hukumar sojin ruwa na kasa Kaptin Suleman Dahun ne ya bayyana haka, Jiya talata, a shelkwatar hukumar da ke Abuja.
Dahun ya bayyana cewa za bayyana dokoki da ka'idojin daukar aikin ne a shafin yanar gizo na hukumar www.joinnigeriannavy.com da za a bude ranar 11-10-2017 domin baiwa mabukatan damar cikewa.
Ya kara da cewa wadanda za su cike dole su zama ainihin haifafun Najeriya, ya kasance Akalla suna da karanci Second Class Upper Division ga masu digiri kenan. Da Upper Credit ga masu HND.
Daractan ya kara da cewa kada tsawon namiji ya kasa mita 1.68, ita kuma mace kada ta kasa 1.65.
Dahun ya cigaba yana cewa dole shekarun mutun kada su wuce 22 zuwa 28 zuwa junairu 31-2018, sai dai wadanda za su nemi Imamai ko wasu bangarori na Musamman kada su haura shekaru 30 zuwa 31 ga watan Junairu na shekarar 2018. (NAN)

