ABUNDA A BA MU FAHINTA BA AKAN KUNGIYAR MURYAR TALAKA.... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 7 November 2017

ABUNDA A BA MU FAHINTA BA AKAN KUNGIYAR MURYAR TALAKA....

Kungiyar Muryar Talaka, Kungiya ce wadda ta kafu da zummar magana da yawon Talaka. Ta yaki azzalumai masu ci da gumin Talaka....
Da dama wasu sukan dauki kungiyar, a matsayin kungiyar da take adawa ko yiwa 'Yan adawa yaki....
Ko daya, ba wata ko wani dan Siyasa da munka rika,  har mu ke kare muradunsa, haka ba jam'iyar da mu ke, kare muradunta....
Akwai abunda mutane sunka ta cewa wai an yi amfani da kungiyar Muryar Talaka an kafa gwamnati amma gwamnatin ta buge da kamun 'Yan kungiyar (A jahar Katsina) A lokacin da anka kama babban Sakataren kungiyar na kasa....
Tabbas haka ne, mun taka rawa matuka wajen sukar lamirin da kuma yayata illar bakin Mulkin gwamnatin da ta gabata. Musamman ganin ta kasa wajen Samar da tsaro a yankin Arewa Maso Gabas. Wanda Alhamdulillahi matasalar yanzu ta yi sauki matuka!
Amma maganar gaskiya ba mu taba yin rubutu ko magana a wani gidan rediyo ko jarida da zummar batawa ko cin mutun wani ko wasu ba. Hakan ma ne ya sa kullum mu ke Kara samun karbuwa, gun talakawan Najeriya. Shuwagabannin da sunka tiki giyar mulki har ta bugar da su kuwa. Sun dauke mu wasu abukkan gabarsu har su ke kokarin tasa mu a gidan YARI.... Da zummar taka muna burki, sai dai kash! Sun yi sake, dan zaki ya girma....
Muna cigaba da fallasa, duk wani azzalamu da ya mayar da dukiyar Talaka a matsayin tashi. Jam'iyarka ko wani naka da kake ganin yana tare da mu duk ba zai yi tasiri a gunmu ba. Mu dai fatanmu a kullum Talaka ya Dara, bakin gwargwado yasan gwamnatin da ya zaba tana tafiya tare da shi.
Ya dan uwa kada ka yi tunanen cewa wannan kungiyar tana yakar azzaluman shuwagabanni ne kurrum, A'a har su kansu talakawa da sunka yi yunkurin tauye hakkin wasunmu, muna shige da fice wajen kwato masu hakkokinsu bakin yinmu....
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I Muryar Talaka reshen jahar Zamfara.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here