LAFIYARTA BUDURWAR KALAU, AMMA TANA BARAN ABINCI A LUNGU DA SAKO NA GARIN GUSAU! YA ZA MU IYA CETO TA? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 8 November 2017

LAFIYARTA BUDURWAR KALAU, AMMA TANA BARAN ABINCI A LUNGU DA SAKO NA GARIN GUSAU! YA ZA MU IYA CETO TA?

Na dade ina mamaki da na ga Wata yarinya wadda za mu iya Kira da BUDURWA Domin shekarunta za su kai sha hudu (14) tana, biyar shago-shago wai a taimaka mata da abinci.

Duk da Dai gaskiya ban samu yin magana ko yi mata kallon kirki ba. amma wadanda sunka wayeta sun tabbatar mani da cewa wannan yarinya ba ta da wata nakasa, wadda ake gani a zahiri ko akasinta.

Kuma ba tun yau su ke ganinta tana baran ba.

Baban abunda ya JA hankalina gareta shi ne;

A Al'adance ban san Mata Suna bara a cikin garin Gusau ba ( Marar Wata na nakasa).

Amma abun mamaki sai yanzu wannan bakar Dabi'ar ta bullo kai.

Ina matsalar take;

Laifinta ko na iyayenta?

Mene ne silar baran?

Wane Hali za ta iya shiga?

Yaushe ta Fara baran?

Ya za iya hanata cigaba da baran tare da dorata akan turbar da za ta iya zama abar alfahari a gaba?

Wadannan tambayiyon ne sunka yi mini tsaye, zan so samun taimkonku. Domin in Allah ya nufi ta dawo Mu taimaka Dan ceto ta.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here