"An aike shi da kudi naira dubu dari biyu 200,000 ya je ya shiga wannan caca ta wasu yan lokutta nan take anka cenye shi kaf! Bayan yafito ne yaje ya saye igiya, wasu daga cikin abokansa sunce ganshi da igiyar amma basu san makasudin sayen igiyar ba. Sai Dai sun ji labarin an ganshi ya rataye kansa."
Wata majiyar kuma tace
Kasuwanci su ke yi shi da uban gidansa, ba tare da sanin uban gidan ba ya dauki dubu 40,000 cikin kudin ya shiga cacar bet9ja, ya fadi. To bai san abinda zai fadawa uban gidansa ba, shi ne ya je ya rataye kansa.
Hakika CACAR BET9JA ta Fara zamarwa matasa masifa Dan Haka hukumomi sai a dauki matakin da ya dace.

