WACE ROMUWA CE MATASHIN JAHAR ZAMFARA YA KE SHA, A GWAMNATIN GWAMNA ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI?? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 1 November 2017

WACE ROMUWA CE MATASHIN JAHAR ZAMFARA YA KE SHA, A GWAMNATIN GWAMNA ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI??

Ranar 1 ga watan 11 ce ranar Matasa da kungiyar hada kan Afrika ta ware domin tunawa da manyan gobenta, tare da kokarin nemawa Matasan nata mafita, akan wasu matsaloli da Matasan su ke fuskanta domin magance su. La'akkari da cewa Matasa su ne kashin bayan cigaban kowa ce Al'umma, Inda har masu iya magana ke cewa; "duk al'ummar da matasanta sunka zama nagari, to Tabbas Al'ummar za ta ci gaba."

Ganin hakan ne kai tsaye sai na hango jahar da nake Rayuwa a cikin, Kasancewar nan ne, mai duka ya halicce ni, wato jahar Zamfara. Domin farawa da gida. Shin wane hali 'Yan uwana Matasan jahar Zamfara mu ke ciki?

Shin gwamnatinmu na kula da mu?

Shin tana ba mu ilimi ingantacce kuma wadacce?

Shin tana yin iya yinta domin nemawa matasa makoma ta gari?

Shin ta kula da yadda mu ke neman abun zaman gari?

Shin dattawanmu da 'Yan siyasarmu sun kula da mu?

Wadannan su ne jerin tambayoyin da na yi wa kaina, tare da yin nitso a kogin tunane domin gano amsarsu, tun daga lokacin da anka damka mulkin jahar ta mu a hannun farar hulla a 1999 zuwa yau . Abunda na tabbatar shi ne gaskiya gwamnatocin da sunka gabata Musamman gwamnatin farar hulla ta farko ta taka muhimmiyar rawa wajen samawa Matasa makoma ta gari, musamman ta bangaren neman ilimi, kirkiro da hanyoyin dogaro da kai ga Matasa da ma musakai, haka ta taka muhimmiyar rawa wajen baiwa kananan 'Yan kasuwa bashi tare da yafe masu in sun turza da biya.

Amma sai kash! Duk da shi gwamna mai ci a yanzu yana cewa wai fa yana koyi ne da mas'habar gwamnan farar hullar Zamfara na farko. Amma kwata-kwata ya watsar da koyarwar da mas'habar baki daya. Musamman wajen taimakawa matasa ta kowane hauji. Idan munka dauki bangaren ilimin Matasa, Rashin daukarsu aiki. Ba a karfafa su. ba ni manta lokacin da wani makaho ya isko ni yana cewa "Dan Allah Abdulmalik ku taimaka ku shedawa Gwamna Shehi cewa, Tun da gwamnatinsa ta hau mulki kwata-kwata bai waiwayo mu ba, duk da bayan ya yi ikirarin cewa mu musakai ne munka saya masa tikitin tsayawa takara a zangonsa na biyi. Har ya yi muna alkawarin zai yi egency Musamman ta musakai domin taimakawa musakai tare ba su Alowace domin yaki da bara, Amma har yanzu bai waiwayo mu ba har 'Yar Santar da mu ke aiki, ciki yau shekaru biyar kenan, kwata-kwata ba kaya. Dan Allah ku taimaka muna neman agaji"

Wannan kenan duk wani mazauni jahar Zamfara ya san an yi shekaru da Rufe babbar cibiyar koyar da matasa sana'o'in hannu da ke Gusau inda dubban matasa ne maza da mata su ke amfana da ita, ta hanyar koyon sana'o'in da za su dogara da su.  Har yanzu ba mu ji an fada muna dalilin Rufe cibiyar ba, duk da alfanun da take da shi ga Matasan jahar Zamfara.

Yau sama da shekaru shida kenan da Rabi da gwamnatin nan ta hau karagar Mulkin jahar Zamfara amma har yau ba ta dauki matashi daya aiki ba, Sai dai korar wadanda ta isko da ta yi bayan ta labe da cewa na bugi ne.

Maganar baiwa matashin jahar Zamfara kwarin guiwar ya tashi ya nemi ilimi kuwa. Har mu matasa mun manta da cewa gwamnatocin jahohin na taimakawa matasa ta hanyar neman ilimi, babu tallafin scholarship har 'Yar Waec da Neco din da daga shekara Sai shekara gwamnati ke biya, an wayi gari Sai dalibbai sun fidda rai daga fitowarta sannan gwamnati ke biya har ta zo gunsu. Wanda hakan kan haifar da tabarbarewar ilimi tare da cilastawa Matasan barin jahar domin neman abun sawa a bakin salati a sauran jahohin Najeriya, wasu Kuma tuni sun zama bakin haure masu hakar ma'adanai ta barauniyar hanya, a kasashe makwabtanmu.

Dan haka ya kamata gwamnatin jahar Zamfara ta yi karatun ta natsu domin waiwayo matasanta, dan wallahi muddun anka tafi a haka duk wani bazamfare Sai ya koka da wannan gwamnati har su masu ci a cikinta yanzu.

Domin za a wayi gari Al'ummar jahar jahilai za su fi rinjaye, Kuma duk inda jahilci ya yi jinjaye dole matsaloli da rashe-rashe kala-kala su yi katoto.

Ku Kuma dattawanmu na jahar Zamfara da sauran 'Yan siyasarmu ya kamata ku farka daga dogon sumar da kunka yi, ku fadima gwamnati gaskiya in ta dauka to, in kuma bata dauka ba daidaikun ku fito da hanyoyin taimakawa matasa Dan taimakon Matasan dama ku kanku

Domin wallahi shirunku illa ce babba ga jahar mu.

Kukan kurciya ne na mu, in an sanya hankali a hankalta, akasin hakan Kuma za a cigaba da yi muna hankakiya.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Matasan Zamfara Ta Tsakkiya) 08069807496

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here