MU 'YAN KASUWAR NAJERIYA! MUNA DA HANNU WAJEN JEFA AL'UMMA CIKIN KUNCIN RAYUWA
A kullum muna Kira ga shugabanninmu da cewa Azzalumai ne, ba su kaunarmu, gurinsu a kullum su bautar da mu tare da jefamu cikin kuncin rayuwa!
Sai dai a bangare daya mukanmu, Azzalumai ne, ba mu kaunar kanmu, muna gurin azabtar da junanmu.
Misali a nan mu 'yan kasuwa daga ranar da munka jiyo labarin kaya za su kara kudi. To daga ranar za mu karawa namu, kudi. Wanda hakan ne, ya sa kusan mafiya abubuwan da sunka kara kudi shekaru biyu Dan karyewar Darajjar Naira. Ba su dawo yadda su ke da ba.
Haka zalika da kayan sun sauka ba ka jin mun rage masu kudi dan tsabar ZALUNCI! Sai lokacin da nagari daga cikin sunka rage kudin.
Mu kalli danbarwar da ke faruwa a halin yanzu cikin Jahar Zamfara. Dare daya masu gidajen ruwa sunka Kara farashin ruwan, Wanda ya cilastawa masu sayarwa daya-daya sunka mayar da su naira 10 a madadin 5 da mu ke saye a baya.
Daga baya wasunsu sunka rage farashin kudin ledar ruwan zuwa naira 70 wanda hakan ya baiwa masu sayarwa damar sayarwa naira 5 biyar.
Sai dai kash! Da yake taron yawa ya fi taron karfi, an cilastawa Wadanda ke sayarwa naira 70 sai sun sayar da su naira 100 wanda hakan ne, ya sanya su shiga Yajin aiki, domin daukar wannan matakin.
Ya kamata mu tashi mu taimaki kanmu, tare da jinkan junanmu . Wanda muddun ba mu yi haka ba, to Wallahi akwai Matsala babba. Haka za mu yi ta wahala, Tun nan duniya lahira kuma Allah ya kyauta.
Allah ya sa mu dace amin, Allah ya ba mu ikon jinkan junanmu.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau Pro 1 Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara.
1-1
1-2017
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Wednesday, 1 November 2017
Home
Unlabelled
MU 'YAN KASUWAR NAJERIYA! MUNA DA HANNU WAJEN JEFA AL'UMMA CIKIN KUNCIN RAYUWA
MU 'YAN KASUWAR NAJERIYA! MUNA DA HANNU WAJEN JEFA AL'UMMA CIKIN KUNCIN RAYUWA
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

