Al'ummar Karamar Hukumar Shinkafi da ke jahar Zamfarar tarayya Nigeria sun su wayi safiyar yau assabar 18-11-2017 da ganin wani Iftila'i na 'Yan Bindiga a wasu kauyukkan Mallamawa da Tunga dake karamar Hukumar ta Shinkafi Inda suka Kashe Sama da mutun ashirin Kamar yanada Rahotanni suka Nuna. Haka zalika maharan sun Kone Gidajen al'umma tare da kone dukiyoyi ba tare da wani Dalili ba.
Matsalar tsaron jahar Zamfara dai ba sabuwar Matsala ba ce, sai Dai an Dan samu sauki matuka bayan. An samu sasanci tsakanin masu tada kayar bayan da da gwamnatin ta Zamfara. Sai dai yanzu matsalar na kokarin dawo wa.



