Hakika idan munka dubi halin kunci da Al'ummar yankin magami, Dansadau su ke ciki. Dole mu tausaya masu matukar gaske!
Wannan yankin yafi karfin Wata karamar hukumar mulkin Jahar Zamfara. Ta fuskar yawan Jama'a da kuma alfanu ga Jahar Zamfara, ganin yankin yana da yabanyar noma tare da albarkatun kasa iri-iri. Wanda hakan ya sa Al'ummar yankin sunka zama 'yan kasuwa na 'Inna-naha, amma fa a shekarun baya. Al'ummar yankin sun yarda da noma da kiyo tare da kasuwancin da sunka yi suna da shi.
Sai Dai kash! Bayan hawan Kan karamar Gwamnati Maici a yanzu. Wannan yankin ya koma kurar-baya, duk wasu ababe da su ke tinkaho da su, sun ja baya. Saboda rashin tsaro, da rashe-rashe da ya yi wa yankin katoto, Domin hatta titunan da mai girma gwamna ya yi suna akai wannan yankin bai samu assasawar daya daga mai girma gwamna ba.
Wanda hakan ya sa, yanzu yankin ya koma Wata karamar gidan yari.
Hujja akan hakan ita ce; Kamar yadda na fada a baya, a Zamfara ba inda ake noma Kamar wannan yankin, amma yanzu saboda matukar rashin tsaron da ke yankin kwata-kwata al'ummarsa sunyi kamfa, mazauna cikinsa da dama sun yi hijira wadanda ke ciki kullum cikin dar-dar su ke rayuwa Haka masu sayar da rai wajen shigarsa. Domin gudun fadama hannun barayin da ke kisan Al'ummar tare da garkuwa da su.
A shekarun baya kasuwar Dansadau tana daya daga cikin Manyan kasuwanin da 'yan kasuwar Najeriya dama yammacin afrika ke hada-hada a cikinta. Amma yanzu kasuwar ta Fara Komawa tamkar kufai, domin ko Al'ummar Zamfara na dar-dar wajen cinta.
Haka zalika tilon titinsu ya yi matukar lalalcewar da za mu iya Kiransa da tarko mutuwa. Domin da wahala ka samu mutun ya shiga yankin da sunan kasuwanci ko wata hada-hada saboda rashin kyawon hanya.
Idan munka dubi bangaren cigaban kasa duk da cewa garin Dansadau yana da basarake mai daraja ta daya (Emir) Wanda hakan ya nuna ba karamin gari ba ne amma Yau kasan shekara hadu 4 kenan Garuruwan Magami da Dansadau rabon su da hasken wutar lantarki wato (Nepa), ba mu maganar DANGULBI, ko Dankurmi Mu ke yi ko wasu garuruwan da ke yankin ba.
Maganar samun tsaftaccen ruwan sha da kayan more rayuwa ma bata taso ba, domin muna tsammanin ma gwamnatin jahar Zamfara ta manta da wannan yankin. Duk da lokacin yakin neman Zabe, ba lungu da Sakon da ba su taka da Kafarsu ba. Da zummar neman goyon baya ga Al'ummar yankin, Wanda Alhamdulillahi sun ci mulkin amma sun manta da su. Wanda ba abunda za mu ce shi ne an ci moriyar ganga kenan an yarda korenta!
Da haka mu ke kira ga ita gwamnatin jahar Zamfara, karkashin jagorancin mai girma gwamna ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI MAFARA. Da ya ji tsoron Allah ya kyautata wannan yankin, ganin cewa suma Suna da hakki da arzikin Jahar Zamfara. Kuma Suna da hakin a kula da rayukkansu fa dukiyoyinsu. Tare da kyautata jin dadinsu.
Daga karshe muna rokon Allah ya sa wannan koken namu ya kai ga kunnuwan mai girma gwamna, tare da ba shi ikon share masu hawayensu.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

