SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR MULKIN TSAFE (HON. ALIYU ABUBAKAR MC) NE GWARZON SHUGABAN KARAMAR HUKUMA, NA ZAMFARA BAKI DAYA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 3 March 2018

SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR MULKIN TSAFE (HON. ALIYU ABUBAKAR MC) NE GWARZON SHUGABAN KARAMAR HUKUMA, NA ZAMFARA BAKI DAYA!


Kamar yadda Kungiyar MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA ta shirya zaben jin ra'ayin jama'a akan Wanda ya dace ya zama GWARZON SHUGABAN KARAMAR HUKUMA, a tsakanin takwarorinsa na Jahar Zamfara.

Hon. Aliyu Abubakar Mc , Tsafe. Bayan ya zama zababben Shugaban Karamar hukumar mulkin Tsafe, an shede shi da kyakkyawan hali da riko da addinin isalama da ma son talakkawan da ya ke cikinsu.

Domin karrama shi tare da kara masa karfin guiwar cigaba da yiwa al'ummarsa ayukkan azo a gani. Wanda Hakan zai kara karfafa takwarorinsa, wajen kula da Al'umma.

la'akkari da wadannan hujjoji kamar haka da al'umma sunka fada akan wannan Shugaba;


BANGAREN ILIMI

✔ Ya Dauki mata 15 yan asalin karamar hukumar mulkin Tsafe zuwa makarantar koyon aikin jinya da unguwar zoma wato (School of nursing and midwifery) Gusau Dan su koyo yadda za su taimaki yan, uwansu mata
..
✔Ya samarwa matasa masu matsalar jarabawa a makarantu dabam-daban a Zacas,Mafara, da makamantasu Dan su gyara Jarabawarsu su ci gaba da karatu.
..
✔ Ya samarwa sama ta MATASA dari biyu 200 gurbin karatu a makarantar kiwaon lafiya dake Tsafe wato (College of health science and technology) haka ya kai wasu makarantar  koyar da fasahar noma da kiyon dabbobi dake bakura (College of agriculture bakura ) ya kai wasu makarantar kere-kere dake Mafara wato (POLY MAFARA)
..
BANGAREN LAFIYA
..
✔Ya inganta asibitin Bilbis
✔Ya inganta asibitin yankuzo
✔Ya inganta asibitin kwaren ganuwa
✔Yanzu haka ana inganta asibitin hayin Alh
✔Ya inganta asibitin gidan dawa
✔Ya inganta Asibitin fegen Dan marka
✔Ya inganta asibitin Bawa ganga
✔ya sawo kayan taimakawa mata masu ciki a asibitin gwamnati dake Tsafe da dai sauransu
..
BANGAREN ADDNININ ISLAMA
✔Ya inganta makarantar islama dake fegin Dan marke
✔Ya inganta babban masallachin yankuzo
✔Ya inganta babban masallachin Cediya
✔Ya Gina masallachi a unguwarshi saboda basuda masallaci a kusa da su
✔Ya bada tallafin naira miliyan daya a makarantar islama dake hadejawa Tsafe da kuma baiwa shugaban makarantar Sabon mashin fill
✔Ya inganta makarantar islama dake gurbin mai komo
✔Ya inganta babban masallacin hayin Sakai.

Da da sauransu.
..
BANGAREN RUWA ABOKIN RAYUWA
..
✔Ya kai ruwan sha Keta
✔Ya kai ruwan sha Kwaren ganuwa
✔Yakai ruwan sha a Dan amana ta galadima
✔Ya bi lungu da sako cikin Tsafe domin gyara borehole Na garin Tsafe da kewaye
..
BANGAREN NAKASASSU
..
✔ ya rabawa guragu kekuna

✔ Ya baiwa makafi tallafi domin su daina bara su kama kasuwanci

BANGAREN MATASA
..
✔Yakai wasu makaranta Dan suyi ilimi

✔Yaraba sama da mashin Dari biyu domin suyi kasuwanci su dogara da kawunansu
✔Ya Raba matasa da dama offer domin su dogara da kawunansu
✔ Ya rabawa matasa filaye dansu yi gini su mallaki muhalli
✔Ya baiwa matasa da dama kudi wasu dubu Dari wasu hamsin wasu dubu Dari biyu duk Dan su kama kasuwanci
..
BANGAREN AYUKKA NA MUSAMMAN
..
✔ Ya ba Alh magaji yandoto kawangilar gadar shemori zuwa hirji dake yandoto ward.
✔Ya ba Alh Nura bello kwangilar renovation Na sakatariya local government
✔Ya Gina tagwayen gadoji guda biyu cikin Tsafe hayin tunbi

✔Ya rabawa yan siyasa motoci

✔Alh Muzakkiru sidi Bawa anbashi 406
✔Alh nasiru amfus henisi
✔Anbaiwa nasui keta kwangila
✔An baiwa boss danjiga kwangila
Da dai sauransu


la'akkari da wadannan kwakkwaran dalillai da kyakkyawan ayukkan nasa. Kungiyar MURYAR TALAKA ta yi Dogaro. Har ta aminta da cewa shi ne ya fi dukkannin takwarorinsa Shuwagabannin Kananan hukumomi a Jahar Zamfara, Dan Haka zata baiwa wannan Dan tahalikin Lambar YABO a Babban taron Kungiyar da za ta yi a watan 3-2018 a Matsayin Kwarzon Shugaban karamar hukuma a Jahar Zamfara.

Muna Taya shi murna, Allah ya ba shi ikon cigaba da yiwa Al'ummarsa abubuwan kirki, muna rokon Allah ya sa wannan kyautar ta kara masa azama. Daga karshe muna rokon Allah ya ba shi Wata kujera da ta fi wannan a 2019 domin cigaba da yiwa Al'umma hidima.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA. A madadin dukkanin shuwagabannin Kungiyar da membobinmu.



Post Bottom Ad

Responsive Ads Here