SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA DAN MAJALISSA MAI WAKILTAR BIRNIN MAGAJI DA KAURA NAMODA (HON. AMINU SANI JAJI) NE GWARZON DAN MAJALISSAR TARAYYA, NA ZAMFARA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 5 March 2018

SAKAMAKON ZABEN JIN RA'AYIN JAMA'A NA MURYAR TALAKA YA NUNA DAN MAJALISSA MAI WAKILTAR BIRNIN MAGAJI DA KAURA NAMODA (HON. AMINU SANI JAJI) NE GWARZON DAN MAJALISSAR TARAYYA, NA ZAMFARA!


Kamar yadda Kungiyar MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA ta shirya zaben jin ra'ayin jama'a akan Wanda ya dace ya zama GWARZON DAN MAJALISSAR a tsakanin takwarorinsa na Jahar Zamfara.
HON. AMINU SANI JAJI Bayan ya zama zababben DAN MAJALISSAR a kananan hukumomin BIRNIN MAGAJI da KAURA NAMODA, an shede shi da kyakkyawan hali da riko da addinin isalama da ma son talakkawan da ya ke cikinsu.
Domin karrama shi tare da kara masa karfin guiwar cigaba da yiwa al'ummarsa ayukkan azo a gani. Wanda Hakan zai kara karfafa takwarorinsa, wajen kula da Al'umma.
la'akkari da wadannan hujjoji kamar haka da al'umma sunka fada akan wannan KANSILA;
1 BANGAREN SAMARWA MATASA AYYUKA
..
✔Jaji Yasamarwa matasa da dama a yankin shi kamar su;
✔Soja
✔DSS
✔Police
✔Costom
✔Prison service
✔ Da hukumomi dabam dabam a matakin kasa wato federal
..
✔BANGAREN TALLAFAWA ADDINI
..
Ya kan bada tallafi suwa ga
✔Masallatai
✔makarantu
✔Walima
✔Maulidi
BANGAREN GINE-GINE
✔ Ya gyara wani dam da ke garin Kuryar Madaro  dake Kaurar Namoda
✔Yanzu haka ana aikin Gina gadoji da kwalbatota cikin kauran namoda
✔Ya Gina makaranta mai Aji uku da dakin Malamai cikin garin Kyambarawa
BANGAREN RUWA ABOKIN RAYUWA
✔Yagina Borehole Billashe Birnin Magaji
✔Ya Gina borehole Gusami-gari
✔Ya Gina Gusami-hayi
✔Kwana kwanan Ya bada naira dubu Dari uku 300,000 a bayan poly kaura domin gyaran fanfunan ruwa dake shiyar.
BANGAREN LAFIYA
✔Lokacin da cutar Amai da zawo ta kunno kai a zamfara ya Dauki mazabun da su kafi kamuwa da wannan cuta guda 8 ya raba masu magunguna  a Kaura da Birnin Magaji
✔Lokacin da ciwon Dan sankarau ya kunno kai ya rabawa duk kusan primary health cares dake yankinsa magunguna dan talakawa su amfana
..
BANGAREN ILIMI
✔Ya rabawa yan yankin shi Na Kauran namoda tallafin karatu wato scholarship mai Degree ko HND dubu coma 10,000 mai Diploma ko Nce dubu biyar 5,000 kuma an bisu makarantunsu kamar Sokoto,Tsafe, Gusau,Kaura, dai dai sauran makarantu.
✔Ya kan kai yayan talakawa makarantu daban-daban dake Nigeria.
BANGAREN ZIYARA KAN LOKACI
✔Jaji ya kanje Daurin aure
✔Ya kanzo jana,iza
✔Ya kan zo walima ko maulidi
..
BANGAREN YAN SIYASA
✔Ya kan kaisuwa MAKKAH
✔Ya kan basu motoci
✔ya kan basu babura
✔ya kan basu kudi.
la'akkari da wadannan kwakkwaran dalillai da kyakkyawan ayukkan, Kungiyar MURYAR TALAKA ta yi Dogaro. Har ta aminta da cewa shi ne ya fi dukkannin takwarorinsa 'Yan majalissar Wakilai na tarayya, a Jahar Zamfara, Dan Haka zata baiwa wannan Dan tahalikin Lambar YABO a Babban taron Kungiyar da za ta yi a watan 3-2018 a Matsayin Kwarzon Dan MAJALISSA a Jahar Zamfara.
Sai HON. ABDULMALIK ZUBAIRU BUNGUDU ya zo na biyu.
Shi kuma
HON. HASSAN DAN IYA, ya zo na uku.
Muna Taya shi Hon JAJI, murna, Allah ya ba shi ikon cigaba da yiwa Al'ummarsa abubuwan kirki, muna rokon Allah ya sa wannan Karramawar ta kara masa azama. Daga karshe muna rokon Allah ya daukaki shi a fagen siyasar domin cigaba da yiwa Al'umma hidima.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA. A madadin dukkanin shuwagabannin Kungiyar da membobinmu.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here