AN DAGE CIGABA DA SHARI'A TSAKANIN MATASA 1400 DA GWAMNATIN ZAMFARA.... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 17 April 2018

AN DAGE CIGABA DA SHARI'A TSAKANIN MATASA 1400 DA GWAMNATIN ZAMFARA....




A yau Talata 17-4-2018 aka yi zama a wata kotu da Matasa sunka Sanya Gwamnatin Zamfara Akan kin biyansu albashinsu da Gwamnatin jahar ta yi bayan ta dauke su aiki Shekaru hudu bata biya su Naira da sunan albashi ba. 


Sai dai ko da aka Kira shariar Matasan  Mai Lamba NICN/KT/02/2017 sai aka sanar da cewa Wakilan gwamnatin jaha da sauran wadanda ake kara ba za su samu damar hallara, a gaban kotu ba.  Saboda haka sun nemi kotu ta sake sa musu rana a duk lokacin da taga ya dace. 


A na shi jawabin, Lauya mai wakiltar maikatan dubu da dari hudu. Ya bayyanawa kotu cewa bashi da masaniyar haka, daga bisani ya nemi cewa kotu ta sanya lokaci mafi kusa domin a cigaba da ssauraren  karar da kuma martanin da bangaren gwamnati suka shigar domin a samu damar gaggauta zartar da adalci ga masu koken.

A yayin nashi jawabin, Alkali E. D. E. Isele ya sanya ranar tara ga watan Mayu domin a cigaba da sauraren karar. 

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here