Cincirindon Matasa NE, sun yi tsinke daga bigiren kasuwancinsu da ke BEBEJI PLAZA, a Babban Birnin jahar ZAMFARA wato Gusau.
Sun yi tsinke zuwa gidan Martaba Sarkin Katsinan Gusau, domin mika kokensu ga Basaraken, akan cin kashin da sunka ce 'yan sanda suna yi masu, Duk da sun rufawa kansu asiri suna kasuwancinsu ba tare da sun dogara da wani ko wasu sun ba su, ko sun zama kangararru ba. A cewar Matasan, sun zo ne domin kokawa ganin cewa shi Sarki shi ne uban kowa, koma kowa dansa NE, Kuma jin maganarsa wajibi ce ga 'ya'yansa.
Da ya maida jawabi Sarkin Katsinan Gusau, Wanda sakataren Masarautar ya wakilta. Ya sha alwashin ganin ce, an sharewa Matasan hawayensu.





